Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 15:33:44    
Kotunan kasar Sin a matakai daban daban na nacewa kan yanke hukunci kan masu laifi da kuma kiyaye hakkin Bil'adama

cri
Ran 10 ga wata, a nan Beijing, Xiao Yang, shugaban kotun koli ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekaru 5 da suka wuce, kotunan kasar Sin a matakai daban daban suna tsayawa tsayin daka kan yanke hukunci kan masu laifuffuka da kuma kiyaye hakkin Bil'adama tare, suna kuma bin ka'idojin yanke hukunci bisa abubuwan shaida a tsanake domin tabbatar da ganin ba a yanke hukunci kan wadanda ba su aikata laifuffuka ba.

Xiao ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ba da rahoton aiki a gun taron shekara-shekara a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta sabon karo. Ya kuma kara da cewa, a cikin shekaru 5 da suka shige, kotunan kasar a matakai daban daban sun yafe wa mutane kimanin dubu 14 da ake tuhumarsu da manyan laifuffuka. Bisa dokoki ne suka tabbatar da ganin wadanda ake tuhumarsu da laifuffuka suna iya daukaka kara. Sa'an nan kuma, mutane kimanin dubu 320 da ake zarginsu da laifuffuka, sun kuma tabbatar da sharadin samun taimakon shari'a sun sami lauyoyin da kotunan kasar suka nada. Yawansu ya karu da ninki sau 2.3 bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.

Kazalika kuma, Xiao ya ci gaba da cewa, a shekaru 5 da suka zarce, kotunan kasar Sin a matakai daban daban sun bi manufofi a tsanake kamar yadda ya kamata kan wadanda suka aikata munanan laifuffuka da kuma wadanda suka aikata laifuffuka marasa muni kwarai.(Tasallah)