Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 16:46:39    
Al'umomin kasashen duniya sun yaba wa jawabin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi kan raya dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan

cri
Ran 4 ga wata, bi da bi ne, al'ummomin kasashen duniya suka yaba wa jawabin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi kan raya dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan.

Ran 5 ga wata, yayin da shugaban kwamitin rukuni mai kula da yanayin duniya da batutuwan Asiya da Pacific na kwamitin harkokin waje na majalisar wakilai ta kasar Amurka, Eni F.F Faleomavaega yake zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, jawabin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi, ya kara baiwa wa mutane kwarin gwiwa, kuma zai yi amfani ga sassauta halin kunci da ke mashigin teku Taiwan.

Ran 6 ga wata, a madadin kungiyar tarayyar Turai, kasar Slovenia, wadda ke shugabancin kungiyar tarayyar Turai, ta ba da sanarwar inda ta nanata cewa, kungiyar tarayyar Turai tana bin manufar kasar Sin daya tak a duk duniya, kuma ta jaddada cewa, "shigar da Taiwan cikin M.D.D ta hanyar kada kuri'ar raba gardama" da hukumar Taiwan ta yi, zai tsananta halin kunci da ke mashigin tekun Taiwan.

Sinnawa a ketare da ke kasar Australia da Thailand su ma sun bayyana cewa, suna nuna tsayayyan goyon baya ga jawabin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi, kuma suna yin adawa da hukumar Taiwan wadda take yunkurin "shigar da Taiwan cikin M.D.D ta hanyar kada kuri'ar raba gardama", suna fatan jama'ar Taiwan da 'yan uwammu na babban yankin kasar Sin, za su yi kokari tare don kawo wa sabon hali ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan.(Bako)