Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 14:46:08    
Hu Jintao ya jaddada babbar manufar Hongkong da Macao da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin take dauka

cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya furta a ran 6 ga wata cewa, maido da Hongkong da Macao a karkashin babban yankin Sin ya tabbatar da cewa, Manufofin gaskiya ne na 'Kasa daya, tsarin mulkin iri biyu', da na 'mutanen Hongkong da na Macao su tafiyar da harkokin su da kansu' yayin da suke cin gashin kansu sosai. 'Yan uwan Hongkong da na Macao suna da basira da karfi wajen ginawa da kula da harkokin Hongkong da Macao, kasar mahaifa za ta ci gaba goyon bayansu har abada.

Hu Jintao ya gana da wakilan jama'a da 'yan kwamitin ba da shawara a fannin siyasa na yankunan Hongkong da Macao wadanda ke halartar tarurukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11 a ran nan a nan birnin Beijing. Inda ya ce, shekarar nan shekara ce ta cika shekaru 30 da aka fara tafiyar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A cikin yunkurin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, 'yan uwan Hongkong da Macao suna takawa muhimmiyar rawa, kuma sun ba da gudummowa sosai.

Kafofin watsa labaru na Hongkong suna mai da martani ga jawabin Hu Jintao sosai, bi da bi ne, suka ba da sharhi a ran 7 ga wata don bayyan ra'ayoyinsu. Jaridun Hongkong da yawa sun bayar da sharhi cewa, Hu Jintao ya yaba wa 'yan uwa na Hongkong da na Macao bisa taimakon da suka bayar , amma mutanen Hongkong ba za su manta ba a cikin shekaru 30 da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, ba ma kawai Hongkong da mutanensa muhimman masu gudanar da wannan aiki ne, hatta ma suna daya daga cikin mutane mafi cin gajiyar wannan manufa. A nan gaba, Hongkong zai kara shiga cikin wannan aikin kasar, da kuma zai mai da hankali sosai wajen raya tattalin arziki. Muddin mutanen Hongkong suka hadin gwiwarsu, to Hongkong zai yi amfani da sabon zarafin bunkasa kasar da samu sabuwar nasara don ba da babbar gudummowa ga kasar mahaifa.(Lami)