Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 13:51:25    
Bangarori daban-daban na kasar Sin sun darajanta muhimman ra'ayoyin shugaba Hu Jintao game da raya dangantakar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan

cri
Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta ruwaito mana labari cewar, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar wanda shi ne shugaban kwamitin soja na tsakiyar kasar Sin Hu Jintao ya yi wani muhimmn jawabi a ranar 4 ga watan da muke ciki kan raya dangantakar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, bangarori daban-daban na kasar Sin sun maida martani sosai ga jawabinsa. Ana ganin cewar, jawabin da shugaba Hu ya yi na da babbar ma'ana kuma zai haifar da tasiri mai zurfi ga gaggauta yin hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan, da jan birki ga aika-aikan 'yan a-ware na yunkurin kawowa kasar Sin baraka, da daukaka cigaban huldar dake kasancewa tsakanin gabobin biyu cikin armashi, tare kuma da sa kaimi ga yunkurin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin ruwan sanyi.

Daraktan reshen kula da harkokin Taiwan na cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta zamani ta kasar Sin Sun Keqin ya ce, muhimman kalaman shugaba Hu Jintao sun shaida cewar, karfin kasar Sin ya samu ingantuwa kwarai da gaske, haka kuma, an fadada da zurfafa cudanya tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan, shi ya sa, mu Sinawa muke cike da imani, mun kara samun wayewar kai. Hakazalika kuma, mun kara samun hankali, da kara sa idao kan hakikanin halin da ake ciki, mun kuma sake nanata cewar, kamata ya yi a kawar da katsalandan daga ketare, da kiyaye zaman lafiya, da cimma moriyar juna tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan. A nasa bangare, shugaba mai bada shawara na kungiyar hadin-kan masana'antun Taiwan dake birnin Shenzhen na lardin Guangzhou Zheng Rongwen ya ce, jawabin da Hu Jintao ya yi ya kara bada kwarin gwiwa ga 'yan kasuwa na Taiwan wajen zuba jari a babban yankin kasar Sin.

A cikin 'yan kwanakin nan, jama'ar Taiwan su ma sun maida martani sosai ga jawabin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi. Yayin da shahararren kwararre, kuma furofesa na jami'ar kimiyya ta Fuying Su Jiahong ke hira tare da manema labarai, ya bayyana cewar, jawabin Hu Jintao ya kirkiro wani kyakkyawan yanayi na bude wani sabon babi wajen raya sabuwar huldar gabobin biyu, ko shakka babu, jawabin zai taka muhimmiyar rawa. Bugu da kari, wakilin musamman na Jaridar Tattalin Arziki ta Taiwan yana ganin cewar, wannan jawabin da shugaba Hu ya yi ya yi nuni da cewar, babban yankin kasar Sin yana aiwatar da manufofinsa kan Taiwan tare da karin sassauci, gaggan shugabannin kasar Sin suna cike da imani kan manufofin da suke tsayawa a kai dangane da batun Taiwan.(Murtala)