Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 21:12:27    
Manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa kan Hong Kong da Macao sun yi daidai sosai, in ji shugaban kasar Sin

cri
Ran 6 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa, abubuwan gaskiya da aka samu bayan da aka komar da Hong Kong da Macao a kasar Sin sun shaida cewa, manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa a wadannan yankunan musamman 2, wato manufar 'kasa daya amma tsarin mulki 2', kuma mazaunan Hong Kong da na Macao suna tafiyar da harkokinsu da kansu, sun yi daidai sosai. Al'ummomin Hong Kong da Macao suna da basira da kuma karfi wajen kulawa da kuma raya Hong Kong da Macao kamar yadda ya kamata. Kasar Sin tana nan kuma za ta ci gaba da mara wa Hong Kong da Macao baya wajen tabbatar da wadata da kwanciyar hankali har abada.

A ran nan da yamma, a nan Beijing, Hu ya gana da mazaunan Hong Kong da Macao masu halartar taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 da kuma taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11. A gun ganawar, shugaban kasar Sin ya ce, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 30 da kasar Sin ta soma yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. Al'ummomin Hong Kong da Macao suna taka muhimmiyar rawa a harkokin yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, suna kuma ba da babbar gudummowa.

Sa'an nan kuma, Hu ya yi fatan cewa, hukumomin Hong Kong da Macao da mutane na rukunoni daban daban za su hada kansu domin mai da hankulansu kan raya tattalin arziki da daukar matakan a-zo-a-gani wajen kyautata zaman rayuwar jama'a da tabbatar da dimokuradiyya sannu a hankali da kuma gama kansu wajen samun jituwa, ta haka za a sami wadata da kwanciyar hankali a Hong Kong da Macao cikin dogon lokaci.(Tasallah)