 Ran 6 ga wata, a nan Beijing, 'yan ci rani 3, wadanda a karo na farko ne suke halartar babban taro na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar koli ta ikon mulkin kasar Sin, sun zanta da manema labaru na gida da kuma na waje tare.
Wadannan wakilai 3 sun zo daga biranen Shanghai da Chongqing da kuma lardin Guangdong, inda aka fi samun mutane masu kaiwa da komowa. Yanzu yawan mazaunan kauyuka 'yan ci rani ya wuce miliyan 200 a kasar Sin. Bullowar wadannan wakilai 3 'yan ci rani ta nuna cewa, a karo na farko ne mazaunan yankuna karkara 'yan ci rani suke iya bayyana ra'ayinsu a cikin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.
A lokacin da suke amsa tambayoyin da manema labaru suka yi musu, wadannan wakilai 3 sun nuna cewa, a shekarun baya, matsayin 'yan ci rani ya sami kyautatuwa sosai, hukumomi na matakai daban daban na kasar sun dauki matakai da yawa domin ba da taimako wajen warware matsalolin da 'yan ci rani suke fuskanta. Sa'an nan kuma, sun bayyana cewa, sharadin jin dadin zama da ba da ilmi ga yaransu da samun tabbacin zaman al'ummar kasa da dai sauransu, batutuwa ne da 'yan ci rani suke fi mai da hankulansu a kai, shi ya sa suna bukatar gwamnatin Sin da ta fi dora muhimmanci a kan wadannan batutuwa.(Tasallah)
|