Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 16:34:56    
Kafofin yada labarai na ketare sun maida hankali kan "Tarurruka Biyu" na kasar Sin

cri

Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, kwanan baya, bi da bi ne kafofin watsa labaru na kasashen waje suka bayar da labarai dangane da "Tarurruka Biyu" da aka yi a nan kasar Sin, haka kuma, sun maida hankulansu sosai kan rahoton aikin gwamnati da firaministan gwamnatin kasar Wen Jiabao ya bayar.

Wasu kafofin yada labarai na kasashen waje ciki har da Jaridar Washington Post, da Jaridar New York Times ta kasar Amurka sun ruwaito kalaman rahoton aikin gwamnati da firaminista Wen ya yi kan cewar, abin dake gaban kome wajen habaka tattalin arzikin kasar Sin shi ne maida hankali kan ingancin bunkasuwa, amma ba saurin bunkasuwa ba ne. Kafofin watsa labarai na Amurka su ma sun bayar da labari na cewar Sin za ta zurfafa yiwa gwamnatinta garambawul, kuma a ganinsu, wannan zai taimaka wajen daidaita sassa daban-daban na gwamnatin Sin, ta yadda za a tinkari batun makamashi da kyau, da inganta kiyaye muhalli, da bada taimako ga aikin yin gyare-gyare kan harkokin kudade.

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta bayar da labari cewar, firaminista Wen ya jaddada cewar, bunkasa tattalin arziki cikin sauri fiye da kima ya riga ya kasance kalubalen tattalin arziki mafi girma a kasar Sin, saboda haka ne, gwamnatin kasar za ta dauki tsauraran matakai domin jan birki ga tsawwalar farashin kaya da zuba jari cikin sauri fiye da kima.

Dadin dadawa kuma, Jaridar Chaosun Ilbo, da KBS da dai sauran muhimman kafofin yada labarai na Koriya ta Kudu sun maida hankulansu kan burin habaka tattalin arziki na wannan shekara da gwamnatin Sin ta tsara, da batun hana hauhawar farashin kayayyaki, da zaman rauywar Sinawa, tare kuma da zurfafa yiwa gwamnati garambawul da sauran makamantansu.

A waje daya kuma, Jaridar Zaobao Daily, da Jaridar Straits Times ta Singapore sun gabatar da rahoton aikin gwamnati da firaminista Wen ya bayar, kuma sun nuna cewar, batun zaman rayuwar al'umma shi ne muhimmin batun dake jawo hankalin gwamnatin Sin.(Murtala)