Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-06 16:21:01    
Kasar Sin tana da aniya da kuma sharadi domin cim ma burin sarrafa farashin kaya

cri

A ran 6 ga wata a birnin Beijing, darektan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Mr Ma Kai ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta samu nasarar daidaita harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni, kasar Sin tana da aniya da kuma sharadi domin cim ma burin sarrafa farashin kayayyaki na shekarar da muke ciki.

A ran 6 ga wata, an kira taron manema labaru na taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11, inda darektan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Mr Ma Kai, da ministan kudi Mr Xie Xuren, da kuma shugaban bankin jama'ar kasar Sin Mr Zhou Xiaochuan suka amsa tambayoyin da aka yi musu kan abubuwan da suka shafi bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da manyan manufofin daidaita harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni.

Mr Ma Kai ya ce, a cikin shekaru 5 na jere, kasar Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki da yawanta ya kai kashi 10, kasar Sin ta kara karfafa ingancin tattalin arziki, da kuma kyautata tsarinsa.

Minista Xie Xuren ya fadi cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan zaman rayuwar jama'a. A cikin shekarar bana, muhimmin sashen kasafin kudi da kasar Sin za ta gudana shi ne, na nuna goyon baya ga aikin gona da kauyuka da kuma manoma, da kuma sha'anin ilmi, sabo da haka ne, yawan irin wannan kasafin kudi zai karu sosai.

Mr Zhou Xiaochuan ya fadi cewa, karuwar darajar kudin Sin yadda ya kamata za ta iya sassauta hauhawar farashin kaya, amma ba za ta iya zama abu mai humimmanci ba wajen sassauta hauhawar farashin kaya ba.(Danladi)