Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 09:55:31    
An bude taron shekara shekara na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri

A ran 5 ga wata da safe a birnin Beijing, an bude taron shekara shekara na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato majalisa ta 11. Shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinglin, da Li Changchun, da Xi Jinping, da Li Keqiang, da He Guoqiang, da Zhou Yongkang da dai sauran shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da na gwamnatin kasar Sin da wakilan majalisar da ya kai kusan dubu 3 sun halarci taron budewa. Shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr Wu Bangguo ya shugabanci wannan taro. Firayin ministan kasar Sin Mr Wen Jiabao ya gabatar da rahoton aiki a madadin gwamnatin da za ta gama wa'adinta a nan gaba ba da dadewa ba, inda aka takaita nasarorin da gwamnatin ta samu a yayin da take tafiyar da harkokin mulki, haka kuma aka gabatar da shawara ga sabuwar gwamnati game da yadda za a gudanar da aikin gwamnati.

A cikin taron da za a shafe kwanaki 13 da rabin ana yinsa, za a dudduba da kuma tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnati, da shirin kasafin kudi, da rahotannin aikin shekara shekara daga taron kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kotun koli ta jama'ar kasar Sin, da Hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin, da kuma shirin yin gyare gyare kan hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

Wa'adin aikin ko wane taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kai shekaru 5, a cikin taro na wannan karo, za a zabi sabuwar gwamnati. Za a zabi shugaban sabon kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da mataimakinsa, da shugaban kasar Sin da mataimakinsa, da shugaban hukumar sojoji ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da kuma tabbatar da jami'an sabuwar gwamnati ciki har da firayin ministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin.(Danladi)