Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 16:40:29    
An bunkasa tsarin dokokin shari'a na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin daga kwarya-kwaryar mataki zuwa sabon matsayi na kama hanya sosai

cri

Ran 4 ga wata, a nan birnin Beijing, kakakin cikakken zama na 1 na majalisar wakilan jama'a a karo na 11 na kasar Sin Jiang Enzhu ya bayyana cewa, an bunkasa tsarin dokokin shari'a na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin daga kwarya-kwarya mataki zuwa sabon mataki na kama hanya sosai.


Jiang Enzhu ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'a na karo na 10 da zaunannen kwamitin majalisar, sun sauke alhakin da kundin tsarin mulkin kasar da dokokin kasar ya dora musu, za su dage kan tsarin majalisar wakilan jama'a da inganta su, da kara ciyar da aikin gina siyasar demokuradiyya ta gurguzu gaba, kuma sun yi aikin matuka, kuma su sami manyan nasarori masu yawa.


Ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'a na karo na 10 ta kara inganta aikin kafa dokokin shari'a a kasar. A cikin shekaru biyar da suka wuce, sun dudduba daftarin kundin tsarin mulkin kasar da daftarin dokokin kasar da daftari kan bayyana dokokin shari'a a kasar da wasu daftarin kudurin da ke shafar shari'a 106, kuma sun zartas da 100 daga cikinsu. Dadin dadawa kuma, majalisar wakilan jama'a ta taka muhimmiyar rawa wajen wakiltar jama'a. A cikin shekaru biyar da suka wuce, wakilai sun gabatar da kudurai fiye da 3700, kuma sun ba da shawara kan kuduri kimanin dubu 30, wasu daga cikinsu sun riga sun zama dokokin shari'a na kasar kuma wasu sun zama abin dogara ne yayin da muka yi wa dokokin kasar gyare-gyare .(Bako)