Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-04 16:18:07    
A tsanake ne, hana samun 'yancin Taiwan na wai da kiyaye zaman lafiya a zirin Taiwan ya zama wani aikin da ya fi muhimmanci kuma ya fi gaggawa a gaban 'yan uwa na gabobi biyu na zirin Taiwan

cri

A ran 4 ga wata a birnin Beijing, kakakin taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta karo na 11 wato Mr Jiang 'Enzhu ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan tana cikin wani halin gaggawa, a tsanake ne, hana samun 'yancin Taiwan na wai da kiyaye zaman lafiya a zirin Taiwan ya zama wani aikin da ya fi muhimmanci kuma ya fi gaggawa a gaban 'yan uwa na gabobin biyu.

Mr Jiang ya ce, aikin sa kaimi ga jefa kuri'ar raba gardama kan shiga cikin MDD da hukumar Chen Shuibian take gudanarwa ya zama wani matakin gaggawa domin neman Taiwan ya samu 'yancin kai bisa doka, wannan aiki kuma ya zama matakin samun 'yanci kai ne da aka canza hanyarsa. Idan an ci nasara, to, tabbas ne zai lalata dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu, haka kuma zai kawo muguwar illa ga zaman lafiya da zaman karko a zirin Taiwan da yankin Asiya da tekun Pacific.

Mr Jiang ya jaddada cewa, ba a yarda da a raba mulkin kai da cikakken yankin kasar Sin ba, ko wane irin batu da ke shafar mulkin kai da cikakken yankin kasar Sin, tilas ne dukkan jama'ar kasar Sin cikin har da 'yan uwa na Taiwan da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 300 sun yanke shawara tare. Muna son yin iyakacin kokari cikin sahihiyar zuciya, domin sa kaimi ga aikin raya dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu cikin lumana, da neman samun makoma mai kyau ta dinkuwar kasar Sin cikin lumana. A sa'i daya kuma, muna shiryawa sosai, domin hana samun 'yancin Taiwan na wai a tsanake, ko kadan ba za a yarda da kowane mutum ya balle Taiwan daga kasar Sin ta kowace hanya ba.(Danladi)