Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 19:10:12    
Sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta bude taron shekara-shekara

cri

Dangane da ayyukan da sabon kwamitin harkokin kasar na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin zai yi a shekaru 5 masu zuwa, Jia ya nuna cewa, dole ne kwamitin harkokin kasar ya mai da hankali kan hadin kai da tabbatar da dimokuradiyya, ya kuma ba da shawara kan harkokin siyasa cikin himma da kyautata tsarin sa ido ta hanyar dimokuradiyya da kuma inganta ba da shawara kan harkokin siyasa.

Burin da Jia ya gabatar ya sami amincewa da dukan mambobin majalisar, Ma Shouxin, wani liman a jihar kabilar Uygur ta Xinjiang mai cin gashin kanta. Ya sake zama mamban majalisar a wannan shekara. Ya gaya mana cewa,'A matsayinmu na mambobin majalisar, mun ji alfahari sosai, haka kuma, mun ji babban nauyi bisa wuyanmu. Za mu kasance tamkar wata gada a tsakanin kabilu daban daban. Za mu koma jihar Xinjiang tare da ra'ayin da aka samu a gun taron, za mu kuma yada shi a ko ina a kasarmu. A sa'i daya kuma mun halarci taron tare da bukatun al'umma da burinsu da kuma wasu batutuwan da ke jawo hankali.'(Tasallah)


1 2