Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 16:46:43    
An soma farkon cikakken zama na sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a nan birnin Beijing

cri

Yau da yamma, wato ranar 3 ga watan Maris, an soma farkon cikakken taro na majalisar ba da shawara kan harkokin siysa ta kasar Sin ta karo na 11 a nan birnin Beijing.

A cikin kowane shekaru 5 an zabi sabbin mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Sabo da haka, wannan ne farkon cikakken zama na shekara-shekara na sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Dukkan manyan shugabannin kasar Sin, ciki har da shugaba Hu Jintao na kasar da firayin ministan gwamnatin kasar Wen Jiabao da shugaba Jia Qinglin na majalisar sun halarci bikin kaddamar da wannan farkon cikakken zama.

A gun bikin kaddamar da taron, Mr. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya ba da wani rahoton aiki a madadin zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta karo na 10 ga mambobi 2195 wadanda suke wakilatar jam'iyyun siyasa iri iri da kabilu da bangarori daban daban.

Mr. Jia ya ce, a cikin shekaru 5 da suka wuce, mambobin majaliasar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin sun sauke nauyin yin shawarwari kan hakokin siyasa da sa ido da ba da shawara kan ayyukan gwamnati ta hanyar dimokuradiyya da ke bisa wuyanta bisa muhimmin aikin da duk kasar Sin take yi. Sun kuma taka muhimmiyar rawarsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasuwanci na gurguzu da harkokin siyasa da al'adu da zaman al'umma na kasar.

Lokacin da yake tsokaci kan ayyukan da majalisar za ta yi a cikin shekaru 5 masu zuwa, Jia Qinglin ya nuna cewa, sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa za ta kara bin ka'idojin hadin guiwa da dimokuradiyya lokacin da suke shawarwari kan harkokin siyasa da kyautata tsarin sa ido ta hanyar dimokuradiyya domin kara kyautatuwar tsarin halarta da ba da shawara kan ayyukan mulkin kasar. Sabo da haka, za a iya sanya majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta bisa tsare-tsare kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)