Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 17:14:08    
Kofofin watsa labaru na Hong Kong suna mai da hankali sosai kan "taruruka biyu"

cri

Ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, an bude taro na shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma za a bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'a a kwana mai zuwa. kofofin watsa labaru na Hong Kong suna mai da hankali sosai kan wadannan "taruruka biyu", kuma suna yin rahotanni kwarai.

A ran 3 ga wata, jaridar "Ta Kung Pao" ta Hong Kong ta kafa filin musamman na "majalisu biyu", inda ta yi rahotanni ga "taruruka biyu". A cikin rahotannin, an gabatar da cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 30 da fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin tana shiga cikin wani zamanin da ke da kyakkyawar siyasa, da zaman rayuwa, da saurin bunkasuwa.

Jaridar "Kasuwanci" ta Hong Kong ta ba da rahoto cewa, yanzu huldar da ke tsakanin babban yanki da Hong Kong tana ta bunkasuwa, yadda wakilan majalisar wakilan jama'a da membobin majalisar ba da shawara na kasar Sin da suka zo daga Hong Kong za su ba da shawara kan bunkasuwar kasa da Hong Kong, da kuma kara taka muhimmiyar rawa kan zaman rayuwa da harkokin siyasa na Hong Kong, wannan zai zama wani abu mafi muhimmanci.