Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 09:55:42    
Jaridar People's Daily ta bayar da bayanin edita domin taya murnar bude zama na farko na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa a karo na 11

cri
Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, da yammacin yau 3 ga wata din nan ne, za a kaddamar da zama na farko na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa a karo na 11. Jaridar People's Daily ta gwamnatin kasar Sin da aka buga a yau ta bayar da wani bayanin edita mai lakabi haka "Inganta hadin gwiwa da cude-ni-in-cude-ka, shimfida siyasa mai dimokuradiyya", domin taya murnar kaddamar da zaman.

Bayanin ya ce, 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa daga jam'iyyu, da kungiyoyi, da kabilu, da bangarori daban-daban sun tattaru tare, domin bada shawarwarinsu kan muhimman harkokin jam'iyyar kwaminis da na kasar Sin, da tofa albarkacin bakinsu kan ayyukan hadin gwiwa da cude-ni-in-cude-ka, da sa kaimi ga harkokin shimfida harkokin siyasa mai dimokuradiyya, da yin tattaunawa tare kan dabarar raya kasar Sin ta hanyar kimiyya. Shirya wannan taro cikin nasara na da babbar ma'ana ga yunkurin tattara hazikancin jama'a, da daukaka cigaban samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, da raya sha'anin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin.

A waje daya kuma, bayanin ya jaddada cewar, tsarin hada kan jam'iyyu da dama da bada shawara kan harkokin siyasa dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wani muhimmin tsarin siyasa ne dake bada tabbaci ga bunkasuwar harkokin jam'iyyar da na duk kasar Sin. Hakikanan abubuwa sun shaida cewar, majalisar jama'a ta bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin tana iya nuna kwarewarta a fannoni da dama, tana kuma taka muhimmiyar rawa, saboda haka ne, ba za a iya maye gurbinta ba. Wannan tsari ya nuna fifikon harkokin siyasa na kasar Sin, kuma wata kyakkyawar dabi'a ce ta siyasa mai dimokuradiyya irin ta gurguzu.(Murtala)