Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-02 21:42:23    
An kammala ayyukan share fage dangane da zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin

cri

A ranar 3 ga wata a nan birnin Beijing, za a bude zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin. A gun taron manema labaru da aka shirya a yau 2 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ba da labaru na taron Wu Jianmin, ya bayyana cewa, yanzu an kammala ayyukan share fage daban daban game da taron.

Mr. Wu ya ce, muhimman ajandun wannan taron ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin suna hade da saurara da kuma dudduba rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar, da halartar taron shekara-shekara na babban taron wakilan jama'ar Sin da za a bude a ran 5 ga wata da kuma tattauna rahoton ayyukan gwamnati bisa matsayin 'yan kallo, da dudduba da kuma zartas da kudurin siyasa na zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin da sauran kudurori da rahotanni.

Majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wata muhimmiyar hukuma ce wadda J.K.S. ke shugabanta wajen yin hadin gwiwa da shawarwarin siyasa tsakanin jam'iyyu da yawa. 'Yan majalisar sama da 2000 za su halarci taron. An ce, za a kawo karshen taron a ranar 14 ga wata. (Bilkisu)