Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-02 20:48:16    
An yi dukkan ayyukan share fage sosai domin zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin

cri

A gun taron manema labaru da aka yi yau ran 2 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, Mr. Wu Jianmin, kakakin ba da labaru na zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin ya yi bayani kan ajandar wannan taron da za yi a nan gaba kadan da kuma ayyukan majalisar, Mr. Wu ya bayyana cewa, yanzu an yi dukkan ayyukan share fage sosai domin wannan taro, kuma za a bude taron bisa lokacin da aka tsayar wato a ran 3 ga wata a nan birnin Beijing. Yanzu ga cikakken bayani game da wannan labari.

Majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wata muhimmiyar hukuma ce wadda J.K.S. ke shugabanta wajen yin hadin gwiwa da shawarwarin siyasa tsakanin jam'iyyu da yawa, kuma wata muhimmiyar hanya ce da ake bi domin yada dimakuradiyya ta gurguzu, wadda ta ba da taimakon da ba za a iya yi mishi tashi in maye ba cikin zaman rayuwar siyasa na kasar Sin.

Tsawon aikin kwamitin duk kasa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa shekaru 5 ne na kowane zagaye, kuma akan kira taro sau daya a shekara. Taron da za a yi a wannan shekara wani babban taro ne da za a kafa sabon kwamitin majalisar ta hanyar yin zabe. Za a shafe kwanaki 11 ga yin wannan taro, kuma da akwai mambobi fiye da 2200 na majalisar za su taru a nan birnin Beijing don yin tattaunawa tare kan harkokin kasar Sin. Wadannan mambobin majalisar suna hade da matanen sassa 34 ciki har da J.K.S. da jam'iyyun dimokuradiyya daban-daban, da wadanda ba su shiga kowace jam'iyya ba, da kungiyoyin jama'a, da kuma kananan kabilu daban-daban. Mr. Wu ya bayyana cewa, "Wani halin musamman na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa shi ne, majalisar tana hade da kwararrun mutane na fannoni daban-daban, sabo da haka majalisar tana da ilmi mai zurfi kuma tana da kwararrun mutane da yawa. Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 11 ta jama'ar kasar Sin ta dauki dimbin sabbin mutane wakilan jam'iyyu da na kabilu da sassa daban-daban, sabo da haka ta bayyana wannan halin musamman na majalisar sosai wato halin wakilci da haduwar kwararru da yawa."

Mr. Wu Jianmin ya kuma bayyana cewa, muhimman ajandun wannan taron ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin suna hade da saurara da kuma dudduba rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar, da halartar taron shekara-shekara na babban taron wakilan jama'ar Sin da za a bude a ran 5 ga wata da kuma tattauna rahoton ayyukan gwamnati bisa matsayin 'yan kallo, da dudduba da kuma zartas da kudurin siyasa na zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 na kasar Sin da sauran kudurori da rahotanni.

Shirin gabatar da ra'ayoyi ya zama wata muhimmiyar hanya ce da mambobin kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ke yi don sauke nauyin da ke bisa wuyanzu wajen shiga da kuma yin shawarwari kan ayyukan mulki. Mr. Wu ya ce, har yanzu mambobin majalisar sun riga sun mika shirye-shiryen gabatar da ra'ayoyi da yawansu ya kai fiye da 300 ga sakatariyar babban taro. Muhimman abubuwan da suka jawo hankulan mambobin sun shafi fannoni 2 wato harkokin kasa da zaman rayuwar jama'a. Mr. Wu ya ce, "Daga wani fanni suna shafi manyan batutuwan yin gyare da bunkasuwa, daga wani fanni daban kuma suna shafi matsalar zaman jama'a wadda take jibintar moriyar jama'a da zaman rayuwar jama'a sosai. (Umaru)