Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-29 17:33:11    
Hu Jintao ya ce, kasar Sin tana son kara raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Nijeriya

cri

A ran 28 ga wata a birnin Beijing, a yayin da shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao yake yin shawarwari da takwaransa na kasar Nijeriya Mr Umaru Musa Yar' Adua, Mr Hu ya ce, gwamnatin kasar Sin tana son kara raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare da ke tsakanin Sin da Nijeriya, kuma bisa tushen zaman daidai wa daida da juna, da moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna, da samun bunkasuwa tare.

Mr Hu ya ce, kafuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare da ke tsakanin Sin da Nijeriya ta tabbatar da sabon makasudi da alkibla domin raya dangantakarsu a cikin sabon karni. Kasar Sin tana son kara raya kyakkyawar dangantakar siyasa da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma kara hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da makamashi, da aikin gona, da manyan ayyuka da fasahohi masu zamani, da kara yin mu'amala a fannonin ala'du da ilmi da kimiyya da fasaha, da horar da ma'aikata masu fasaha ga kasar Nijeriya.

Mr Yar' Adua ya sake nanata cewa, gwamnatin kasar Nijeriya tana tsayawa kan manufar kasar Sin daya, tana nuna goyon baya ga babban sha'anin dinkuwar kasar Sin. Ya ci gaba da cewa, kasar Nijeriya tana maraba da kamfanonin kasar Sin domin gudanarwa da ayyukan wutar lantarki da sadarwa da hanyoyin jirgin kasa da albarkatun mai da gas a kasar.

A ran nan kuma, firayin ministan kasar Sin Mr Wen Jiabao kuma ya gana da Mr Yar' Adua.(Danladi)