Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-29 15:30:38    
Bayani kan gasar wasannin Olympics na London

cri

Aminai masu sauraro, ko kuna sane da cewa, an samu damar gudanar da gasar wasannin Olympics ta hudu ta shekarar 1908 a London ne duk bisa tallafin da hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta Londan ta yi. Amma, duk da haka, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da kuma Mr. Pierre Coubertin ba su yi hakuri da hakan ba domin ba su ji dadi da yadda aka gudanar da gasannin Olympics sau biyu kafin wannan a karkashin inuwar hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta duniya. Amma, abun da ya wuce tsammaninsu, shi ne an cimma nasara a gun gasar wasannin Olympics da aka gudanar a wannan gami, wadda ta sha bamban da nasarorin da aka samu a da duk bisa hadin gwiwar da aka yi tsakanin kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da kuma hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta duniya.

Bisa aiki tukuru da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta London ya yi, gasar wasannin Olympics ta London a shekarar 1908 ba ta gamu da cikas da tasiri daga hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta duniya ba in ban da dan tsawaita lokaci kadan da aka yi na gasar din. A lokaci guda, an gane cewa, muradin hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta duniya na tallafa wa kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, shi ne domin daukaka kwarjinin al'ummar Burtaniya ba wai domin manufar kasuwanci ba. Hakan ya janyo jin dadi ga hadin gwiwar da aka yi a wannan gami.

Kwamitin shirya wasannin Olympics na London ya yi amfani da kudaden da hukumar kula da harkokin baje-kolin kayayyaki ta duniya ta bayar wajen gina wani babban filin wasan motsa jiki, wanda ke iya daukar 'yan kallo da yawansu ya zarce 70,000. Lallai abun al'ajabi ne aka samu a wancan lokaci. Wannan babban filin wasa ya kasance tamkar wani muhimmin wuri, inda ake yin farfaganda kan wasannin motsa jiki na zamanin yanzu. Ban da wannan kuma, wannan babban filin wasa ya samar wa 'yan kallo wani dakalin kallo da aka gina da bakin karfe. Wannan dai, wani kirkiro ne da ba safai akan ga irinsa ba a tarihin gine-ginen wasannin motsa jiki. Bisa labarin da muka samu, an ce, akwai kuma kirkire-kirkire da dama masu ma'anar ishara da aka yi a gun gasar wasannin Olympics ta London a shekarar 1904:

Da farko, kwamitin shirya wasannin Olympics na London ya yi kwaskwarimar ka'idoji kan gasanni da dama musamman ma wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Har wa yau dai, akan yi amfani da wadannan gyararrun ka'idoji da yawa a gun gasa.

Ban da wannan kuma, karo na farko ne 'yan Burtaniya suka kaddamar da salo iri daya na tufafin 'yan wasa na kasashe daban-daban da suka sanya a gun bikin bude gasar, inda suka zagaya filin wasan sau daya rike da tutar mulkin kasarsu ko kuma ta yankinsu, daidai kamar yadda akan yi har yanzu.

Dadin dadawa, yawan kasashe da yankuna da suka shiga gasar wasannin Olympics ta London ya kai 22, 'yan wasa ma sun kai 2,034 wato ke nan a karo na farko ne yawan mutanen da suka halarci wata gasar wasannin Olympics ya zarce 2,000 a cikin tarihin wasannin Olympics. A ciikinsu, 'yan wasa mata ya kai 36. Ko da yake su kalilan ne, amma wannan ya shaida cewa, yawan 'yan wasa mata dake halartar gasar wasannin Olympics na karuwa a kwana a tashi. ( Sani Wang )