Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 15:01:46    
Kasar Sin amintacciyar kawa ce ga tarayyar Nijeriya

cri
Kwanan baya, ministan harkokin wajen tarayyar Nijeriya Ojo Maduekwe ya bayyana a birnin Lagos cewar, kasar Sin wata amintacciyar kawa ce ga Nijeriya. Ziyarar da shugaban kasar Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua zai kawowa kasar Sin nan ba da jimawa ba za ta inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake kasancewa tsakanin Nijeriya da Sin.

Mr. Maduekwe ya yi wannan furuci ne yayin da yake hira tare da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, a gabannin ziyarar shugaba 'Yar Adua a Sin. Ya ce, "cikin sahihanci ne kasar Sin take taimakawa kasar Nijeriya da sauran kasashen Afirka wajen habaka tattalin arziki, musamman ma ta fuskar shirya dandalin fadi-sonka kan hadin gwiwar Sin da Afirka, gwamnatin kasar Sin tana cigaba da samarwa kasashen Afirka tallafin kudi da na fasaha, saboda haka ne, bangaren Nijeriya ya nuna yabo sosai gare ta."

Mr. Maduekwe ya kara da cewar, Nijeriya za ta cigaba da maida hankalinta da koyon nasarorin da kasar Sin ta samu, haka kuma, za ta fadada hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni daban-daban, ciki har da fasahohi, da zirga-zirga, da sha'anin noma, da kuma manyan ababen more rayuwar jama'a. Nijeriya za ta samu alfanu daga dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raya sha'anin noma na zamani, haka kuma, za ta kara samun kudi daga masana'antun da ba na man fetur ba.

Mr. Maduekwe ya kuma jaddada cewar, Nijeriya ta dade tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duk duniya, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi ba daga kasar Sin, gwamnatoci daban-daban na tarayyar Nijeriya dukkaninsu sun rufawa gwamnatin kasar Sin baya wajen warware batun Taiwan a karkashin wannan ka'ida. A waje daya kuma, Maduekwe ya bayyana cewar, a ganin gwamnatin Nijeriya, bai kamata ba a hada gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da harkokin siyasa. Gwamntin Nijeriya ta amince cewar, kasar Sin tana iya karbar bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta Oympics ta Beijing da kyau kuma cikin nasara.(Murtala)