
Ran 21 ga wata, cibiyar ba da umurni cikin gaggawa ta jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki da fama da bala'i ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, zuwa ran 20 ga wata da karfe 11 da dare, an farfado da samar da wutar lantarki ga jiragen kasan da suke yin amfani da wuta da aka katse sabo da bala'i a yankunan da ke layukan kudancin kasar Sin.
Zuwa ranar 20 ga wata da karfe 5 da yamma, an farfado da layukan wutar lantarki da suka katse sabo da bala'in a dukkan kasar da yawansu ya kai kashi 83 cikin kashi 100, haka kuma an farfado da kashi 88 cikin kashi 100 na tashoshin injunan rarraba wutar lantarki da suka katse sabo da bala'in.

Ran 21 ga wata, jiragen kasa da motoci da jiragen sama dukkansu sun kama aiki yadda ya kamata, yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta jiragen kasa da motoci sun ci gaba da yin kasa-kasa.
Ran 21 ga wata, an rage farashin kayan lambu a kasar Sin, a wasu yankunan, farashin ya ragu sosai.(Bako)
|