Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 12:38:29    
Yawan wutar lantarki da ake samu a yankunan kasar Sin masu fama da bala'u ya kai matsayi yadda ya kamata sannu a hankali

cri

Bisa labarin da muka samu daga cibiyar ba da jagoranci wajen jigilar kwal da wutar lantarki da mai, da yaki da bala'u na majalisar gudanarwa ta kasar Sin a ran 20 ga wata, an ce, kasar Sin ta riga ta maido da aikin samar da wutar lantarki a gundumomi 90 da ke kudancin kasar Sin, wadanda aka dakatar da samar musu wutar lantarki sakamakon bala'un dusar kankara. Yawan wutar lantarki da aka samu a yankunan kasar Sin da ke fama da bala'u ya kai matsayin yadda ya kamata sannu a hankali.

A ran 20 ga wata, kasar Sin tana gudanar da aikin jigila na hanyoyin jiragen kasa, da na motoci, da jiragen sama yadda ya kamata. Cikin babban mataki ne, aka samar da wutar lantarki da kwal. Farashin kayayyakin lambu da nama ya ci gaba da saukawa a wuraren da bala'in ya shafa.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa ranar 19 ga wata, kasar Sin ta kebe kudi da bayar da rancen kudi da yawansu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 76 don yaki da bala'in.(Danladi)