Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-19 13:47:14    
Gwamnatin kasar Sin ta bukaci hukumomi na matakai daban-daban na kasar da su yi kokari wajen maido da ayyukan tushe a wuraren da bala'in ya shafa

cri

Kwanakin nan, gwamnatin kasar Sin ta ba sanarwa cewa, ya kamata hukumomi na matakai daban-daban na kasar su ci gaba da inganta jagorancinsu, kuma su yi shiri cikin tsanaki, kuma su jagoranci kwadago, da kayayyaki da kuma dukiyoyi daga manyan fannoni, don gaggauta maido da ayyukan tushe a wuraren da bala'in ya shafa, kuma a yi kokari wajen maido da sha'anin gona, da kiyaye zaman rayuwar jama'a a wuraren da bala'in ya shafa, da gaggauta sake shimfida zaman doka da odar a cikin zaman rayuwar jama'a da kuma aikin kawo albarka, don a yi kokarin rage yawan hasarorin da bala'in ruwan sama da dusar kankarar da suka kawo.

Cibiyar ba da umurnin cikin gaggawa ta jigilar man fetur da kwal da wutar lantarki ta majalisar gudanarwa ta Sin ta tsaida matakai da za a dauka, wadanda suka hada da: a yi kokari wajen gyaran ayyukan tushe da suka lalace, da gaggauta maido da sha'anin gona, kuma inganta kiyaye jigilar man fetur da kwal da wutar lantarki, da kuma a tabbatar da zaman rayuwar jama'a da ke wuraren da bala'in ya shafa, da kuma a sanya karfi wajen rigakafin sake barkewar bala'in a wurin.

Bisa labarin da muka samu, ya zuwa yanzu jiragen kasa da motoci da kuma jiragen sama sun kama aiki yadda ya kamata. Masana'antu da yawansu ya kai kashi 94 cikin kashi 100 da kuma kashi 90 cikin kashi 100 na gidajen da aka samu katsewar wutar lantarki sabo da bala'in a kudancin kasar Sin, yanzu dukkansu sun maido da samar da wutar lantarki cikin armashi. Farashin kayan lambu da kwai da nama da ke wuraren da bala'in ya shafa, sun yi kasa-kasa, amma farashin man girki da abinci sun ci gaba da zaunar da gindinsu.(Bako)