Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-18 15:08:35    
Ana bunkasa sana'o'i daban daban don kara wa manoma kudin shiga a lardin Liaoning na kasar Sin

cri

A cikin shekarun nan da suka wuce, ta hanyar bunkasa sana'o'i daban daban, manoma sun kara samun kudin shiga mai yawa a wurare daban daban na lardin Liaoning da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Yanzu kuma kananan hukumomi na lardin suna kara kokari wajen bunkasa sana'o'i daban daban don kara wa manoma kudin shiga mai yawa.

A cikin wani dogon lokaci da ya wuce, manyan masana'antu su ne ginshikan tattalin arzikin lardin Liaoning ne. A cikin shekarun nan da suka wuce, gwamnatin lardin ta ba manoma kwarin gwiwa wajen bunkasa sana'o'i daban daban don cim ma manufar bunkasa aikin masana'antu da na noma cikin daidaituwa kuma kamar yadda ya kamata. A wani kauye mai suna Dalishu na lardin, dukkan manoma sun sami arziki ne ta hanyar bunkasa tattalin arziki cikin hadin gwiwa.

Da ganin cewar yanayin kasa ba shi da kyau a kauyensu da ke kan tudu, sai manoma suka kafa wani babban lambun itatuwa masu ba da 'ya'ya mai fadin kadada 1800 a kauyen Dalishu cikin hadin gwiwa, don haka yanzu masu yawon shakatawa da yawa na zuwa kauyensu don cire 'ya'yan itatuwa da sauransu a ko wace shekara. Bayan haka Manoma sun gina otel-otel da cibiyoyin taruruka da filin wasan kwallon kwando da gidan cinima da sauransu don neman kara samun kudin shiga mai yawa daga wajen harkokin yawon shakatawa.

Yanzu, iyalan manoma sama da 400 a kauyen Dalishu sun riga sun gina kyawawan gidajensu masu benaye, sa'an nan iyalan manoma sama da 40 sun sayi kananan motocinsu. Manomi Li Qingzhong yana daya daga cikinsu. Da ya tabo magana a kan arzikin da suke samu ta hanyar bunkasa tattalin arziki cikin hadin gwiwa, sai ya bayyana cewa, "iyalina yana da mutane 6, matsakaicin yawan kudin shiga da ko wanensu ke samu a ko wace shekara ya kai kudin Sin Yuan dubu 20 zuwa dubu 30 daidaita kimanin Naira dubu 280 zuwa dubu 420. Yanzu, fadin gonaki da iyalina ke mallaka ya kai kimanin kadada 4. A farkon lokaci, na noma kayayyakin lambu da itatuwa masu ba da 'ya'ya, daga baya na noma tsire-tsire da ake amfani da su wajen hada magungunan sha iri na gargajiyar kasar Sin. Yanzu na sami arziki, na sayi mota kuma na gina gidada kaina."

Manomiya Guan Xin ta kauyen Dalishu wadda ta riga ta sami arziki sosai ta bayyana cewa, "iyalina yana da mutane hudu, matsakaicin yawan kudin shiga da ko wannenmu ke samu ya kai kudin Sin Yuan dubu 20 daidai da kimanin Naira dubu 280 a ko wace shekara. Na sayi motoci hudu masu daukar kaya, wadanda nake amfani da su wajen jigilar kayayyaki domin kauyenmu da sauran wurare. Kudin shiga da nake samu daga wajensu ya kan yi yawa a ko wace shekara."

Manomi Mao Fengmei, jami'in hukumar kauyen Dalishu yana ganin cewa, bunkasa tattalin arziki cikin hadin gwiwa wata muhimmiyar hanya ce da manoma ke bi don samun arziki. Ya ce, "a ganina, bunkasa harkokin tattalin arziki cikin hadin gwiwa musamman na kauyuka yana da muhimmanci sosai. Yanzu, mun riga mun sami babban ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinmu, tabbas ne, makomarmu za ta kara kyau. Manufar da muke son cimmawa ita ce kara jin dadin zamanmu har fiye da yadda mazaunan birane ke yi. "

Manomi Mao Fengmei ya kara da cewa, a cikin shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta fito da manufofi game da tallafin aikin noma, kuma ta kashe makudan kudaden jari wajen bunkasa aikin noma. A gun babban taron wakilan kasa na karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, an gabatar da manufofi da dama don kara ba da taimako wajen raya kauyuka, shi da sauran manoman kauyensa sun ji farin ciki da kwarai, kuma sun hakkake cewa, manoman kasar Sin za su kara samun fa'ida daga wajen ci gaban da ake samu wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.(Halilu)