
Ya zuwa ran 13 ga wata, kasar Sin ta rigaya ta tura rukunonin ba da jiyya da rigakafi da sa ido kan ayyukan kiwon lafiya dubu 25 ko fiye zuwa yankunan dake fama da bala'in dusar kankara, wadanda suka hada da likitoci fiye da dubu 180.

Wakilinmu ya samu wannan labari ne a ran 13 ga wata a cibiyar ba da umurni ga aikin sufurin kwal da wutar lantarki da aikin yaki da bala'i ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin.
Bugu da kari, yawan mutanen da suka ji rauni ko ke fama da bala'in da wadannan likitoci suka ceto ya wuce dubu 400, kuma sun ba da magunguna da kayayyakin jiyya da yawansu ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 13.
|