Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-13 20:14:59    
Gwamnatin kasar Sin na yin ayyukan sake raya wurare masu fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara

cri

Yau 13 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya shugabanci taron zartaswa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, domin nazari da kuma shirya ayyukan sake raya wurare masu fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara.

Taron ya nuna cewa, an samu nasara sosai bisa mataki wajen ayyukan fama da karanci, da ruwan sama da dusar kankara. Yanzu an riga an mai da harkokin sufuri a dukkan kasar kamar yadda ya kamata, kuma an gama ayyukan gyara yawancin layukan samar da wutar lantarki da suka lalata, da tashoshin samar da wutar lantarki, kazalika an mai da aikin samar da wutar lantarki wajen zaman rayuwar mazuna wurare masu fama da bala'in kamar yadda ya kamata, bugu da kari kuma ana ta kara yawan kwal da ake adanawa a kamfannonin samar da wutar lantarki. Bayan haka kuma, an sake tsugunar da jama'a masu fama da bala'in cikin lokaci, kuma tsarin zaman takewar al'umma yana tafiya kamar yadda ya kamata.



A gun taron, an jaddada cewa, a mataki nan gaba, za a mai da hankali kan sake raya wurare masu fama da bala'in a dukkan fannoni.

Bayan haka kuma, an samu labari a wannan rana cewa, ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta kasafta kudin Sin yuan miliyan 20, don yin amfani da fasahohin da abin ya shafa da kuma yada-da su wajen sake raya wurare masu fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara a kudancin kasar. (Bilkisu)