Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-13 19:18:35    
An kafa cibiyar hana satar fasahar dabi a kasar Sin

cri

Yanzu, a nan birnin Beijing, hukumar kula da ikon mallakar dabi ta kasar Sin ta kafa wata cibiya domin gabatar da rahoton tonon laifufukan satar fasahohin dabi wato cibiyar za ta rika karbar rahotannin da jama'a suka gabatar a kan laifufukan harar ikon mallakar kayayyakin dabi da satar fasahohin dabi. Shugaban babbar hukumar kula da ayyukan watsa labaru da aikin dabi kuma shugaban hukumar kula da ikon mallakar dabi ta kasar Sin Mr Liu Binjie ya bayyana cewa, aikin zai jagoranci jama'ar rukunoni daban daban da ke zamantakewar al'umma da su shiga ayyukan yaki da laifufukan satar fasahohin dabi ta hanyar aikin kasa, domin yin haka na da ma'ana sosai.

Kwanan baya ne aka kammala kafa cibiyar karbar rahoton tonon laifufukan satar fasahohin dabi ta hukumar madaba'a ta kasar Sin a nan birnin Beijing, jami'an kungiyar kiyaye ikon mallakar ilmi na kasa da na babbar hukumar madaba'ar kasa da na cibiyar kiyaye ikon mallakar fasahohin dabi ta kasa da wakilai na kungiyar tarayya ta kula da ikon wallafe wallafe da abin ya shafa a cikin gida da wakilan kungiyar masu rike da ikon mallakar kayayyakin dabi na kasashen waje sun halarci bikin kafuwar. Wata malama mai suna Xiang Xin wadda ita ce jami'ar ofishin kungiyar mai kula da ikon mallakar ilmi ta kasar Sin ta bayyana cewa, kafawar cibiyar ta bayyana niyyar gwamnatin kasar Sin game da ci gaba da yaki da satar fasahohin dabi, ta bayyana cewa, wannan aikin wata dawainiyar gwamnatin kasar Sin ce dangane da aikin kiyaye ikon mallakar ilmi a shekarar 2007. Kafa irin cibiyar rahotannin tonon laifufukan satar fasahohin dabi ci gaba ne da bayyana niyyar gwamnatin kasar Sin da matsayinta wajen yaki da laifufukan satar fasahohin dabi da kiyaye moriyar masu wallafe-wallafe bisa shari'a.

Cibiyar ta sanar da lambar wayarta wato 12390 da adireshinta a internet wato (Jubao @ncac.gov.cn) don karbar rahotannin tonon laifufukan satar fasahohin dabi da jama'a suka gabatar daga zamantakewar al'umma, kuma tana da nauyin bayar da yabo ga wadanda suka ba da gudumuwa wajen gabatar da rahoton tonon laifufukan satar fasahohin dabi.

Don kara karfin yaki da laifufukan satar fasahohin dabi wadanda suka kawo barna sosai ga fa'idar jama'a , hukumar ta kuma samar da kudade don nuna yabo ga wadanda suka ba da gudumuwa ga tonon laifufukan satar fasahohin dabi.

Mr Liu Binjie ya bayyana cewa, kafa cibiyar na da ma'ana sosai. Ya bayyana cewa, kasa ta kafa cibiyar, kuma ta samar da kudadde don nuna yabo ga wadanda suka ba da gudumuwa ga tonon laifufukan satar fasahohin dabi, kuma ana yin jagorancin ayyukan yaki da irin wadannan laifufuka ta hanyar aikin kasa da samar da kudaden yabo, jama'a farar hula kuma su ma su shiga aikin yaki da irin wadannan laifufuka. A wani fanni, an tayar da himmar jama'a don shiga aikin yaki da irin wadannan laifufuka, a wani fanni daban kuma, ta hanyar ayyukan, ana iya sanar wa zamantakewar al'umma da karfi sosai cewa, satar fasahohin dabi aiki ne na yin laifufuka, ta hakan, za a iya hana samun laifufukan satar fasahohin dabi.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da yawa don yaki da laifufukan satar fasahohin dabi, saboda haka ta sami yabo daga kasashen duniya.

Mr Liu Binjie ya ci gaba da bayyana cewa, a wani fanni, wajen yaki da laifufukan satar fasahohin dabi, ya kamata a dogara bisa karfin shari'a da kuma dogara bisa aikin da hukumomin gwamnati suka yi wajen aiwatar da dokokin shari'a, amma a karshe dai in ana son daidaita matsalolin satar fasahohin dabi, to dole ne a dogara bisa karfin jama'a.

Saboda haka matakin kafa cibiyar yaki da laifufukan satar fasahohin dabi ya sami goyon baya da yabo daga wadanda suke da ikon wallafe-wallafe.

Mr Liu Binjie ya kuma bayyana cewa, dukkan mutane na kasar Sin ko na kasashen waje ko kungiyoyin jama'a ko a gida ko a waje, dukkansu suna iya samun lambar yabo bisa sakamakon ba da gudumuwa wajen gabatar da rahotannin tonon laifufukan satar fasahohin dabi, yawan kudin yabo zai kai kudin Sin Yuan dubu 100. (Halima)