Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-12 18:14:24    
Sinawa suna jin dadin tsaron hutu domin murnar bikin bazara

cri

Yau, ran 12 ga wata, rana ta karshe ta tsawon hutu na kwanaki 7 domin murnar bikin bazara na kasar Sin. Lokacin da ake murnar wannan bikin gargajiya mafi muhimmanci a nan kasar Sin, Sinawan da suke da zama a wurare daban-daban, ko sun kai ziyara ga dangogi da abokansu, ko iyalai sun taru tare, ko sun yi yawon shakatawa a wurare daban-daban. A wasu yankuna masu fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara da ke kudancin kasar Sin, bisa kokarin da gwamnati da jama'a suka yi tare, fararen hula sun gudanar da murnar bikin bazara kamar yadda ya kamata.

Shan iska a gun bukukuwan wasannin nishadi na gargajiya na daya daga cikin wasannin nishadi da Sinawa suke yi lokacin da suke murnar bikin bazara. A nan birnin Beijing da lardin Jilin da birnin Shenyang da birnin Tianjin da birnin Jinan na lardin Shandong da birnin Changsha na lardin Hunan da birnin Nanjing na lardin Jiangsu, an shirya bukukuwan wasannin nishadi na gargajiya iri daban-daban da ke bayyana al'adun musamman na wurare daban-daban.

A gun bikin wasannin nishadi da aka shirya a dakin ibada na Tiantan da ke birnin Beijing, an yi nune-nunen abubuwan tarihi na al'adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni fiye da dubu 1da ke bayyana tarihin birnin Beijing. A waje daya kuma, an kebe wani fili domin nune-nunen wadannan abubuwan tarihi. Ko mazauna birnin Beijing, ko masu yawon shakatawa da suka zo Beijing daga sauran wuraren kasar Sin sun yaba wa wannan biki kwarai.

Wata mace mai yawon shakatawa ta ce "Abin al'ajabi ne. Ina jin dadin kallonsu."

Wani namiji mai yawon shakatawa ya kuma ce, "Da kyau, abin mamaki ne"

Ba ma kawai ana shirya bukukuwan wasannin nishadi ba, har ma ana wasa da aman wuta da fili-fili domin murnar bikin. A birnin Weifang na lardin Shandong, mutane wadanda suke da sha'awar wasan fili-fili suna farin ciki sosai domin suna murnar biki ne ta hanyar wasan fili-fili. Mr. Zhang Xiaodong, wani mazaunan birnin Weifang ya ce, "Wannan lokacin murnar bikin bazara ne. Dukkanmu baba da yara mun zo nan mun yi wasa da fili-fili domin jin dadin bikinmu. Muna fatan fili-filinmu za su tashi cikin sararin sama, zaman rayuwarmu zai kara samun kyautatuwa."

Kafin Sinawa mu shiga lokacin murnar bikin bazara, wani bala'in ruwan sama da dusar kankara ya bullo a wasu yankunan da ke kudancin kasar Sin ba zato ba tsammani. Ya kuma katse zirga-zirga da wutar lantarki a wasu yankuna. Ba a iya samun ruwan sha da wutar lantarki da abinci da kayan lambu kamar yadda ya kamata ba. Sabo da haka, hukumomin gwamnati na wurare daban-daban sun dauki matakai sun taimaki jama'a masu fama da bala'in da su taya murnar bikin bazara cikin fara'a.

A lardunan Zhejiang da Guangdong, inda ke da dimbin 'yan cirani, 'yan ci rani ba su iya komawa garinsu domin murnar bikin bazara tare da iyalansu ba sakamakon bala'in ruwan sama da dusar kankara. Sabo da haka, gwamnatoci da masana'antu na wuri sun shirya musu abinci da wuraren kwana da bukukuwan al'adu. Yarinya Peng Ting, wata 'yar lardin Guizhou wadda take aiki a lardin Zhejiang ta ce, "Ko da yake ba mu iya komawa garinmu ba a wannan lokacin murnar bikin bazara, amma ina kuma farin ciki sosai a nan lardin Zhejiang. Ina fatan garinmu zai samu kyautatuwa cikin sauri."

Bayan da aka samu bala'in ruwan sama da dusar kankara a wasu yankunan kudancin kasar Sin, bangarori daban-daban na al'ummar kasar sun samar wa jama'a masu fama da bala'in taimako da kayayyakin jin kai da yawansu ya riga ya kai fiye da kudin Renminbi yuan biliyan 1 ya zuwa ran 11 ga wata da dare.