 Ya zuwa yanzu, ana gudanar da harkokin zirga-zirga a lokacin murnar bikin bazara na kasar Sin da kuma ayyukan ceto a yankuna masu fama da bala'in dusar kankara kamar yadda ya kamata.
A ran 11 ga wata da karfe 8 da yamma, cibiyar ba da umurni cikin gaggawa ta jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki da fama da bala'in dusar kankara ta kasar Sin ta sanar da sabon ci gaba da duk fadin kasar ta samu wajen fama da bala'in.

Ya zuwa ran 11 ga wata da karfe 3 da yamma, ana amfani da hanyoyin motoci masu saurin tafiya da muhimman hanyoyin dogo na kasar Sin yadda ya kamata, ban da wasu hanyoyin da ke cikin lardunan Hunan da Yunnan da aka rufe sakamakon kankara. Haka kuma ana tafiyar da harkoki a filayen jiragen sama na fasinja na duk kasar yadda ya kamata. A yankunan da ke fama da bala'in, yawancin larduna sun riga sun samar da wutar lantarki kamar yadda ya kamata. Yanzu sojojin kasar Sin suna ci gaba da samar da taimako wajen fama da bala'in, kuma an samu daidaito wajen farashin kayayyaki na kasuwannin yankuna masu fama da bala'in.(Kande Gao)
|