Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-11 17:43:10    
Ba a samu bullar manyan matsalolin kiwon lafiyar jama'a ba a yankunan da ke fama da bala'in dusar kankara na kasar Sin

cri

Wakilinmu ya samu labari a ran 10 ga wata daga cibiyar ba da umurni cikin gaggawa ta jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki da fama da bala'in dusar kankara ta kasar Sin, cewa ya zuwa yanzu, ba a samo bullar manyan matsalolin kiwon lafiyar jama'a ba a yankuna masu fama da bala'in ruwa da dusar kankara.

Kuma an labarta cewa, ya zuwa ran 10 ga wata, hukumomin kiwon lafiya na yankunan da ke fama da bala'in sun aika da kungiyoyi fiye da dubu 23 wajen yin jiyya da shawo kan cututtuka da kuma sa ido kan ayyukan kiwon lafiya, da ma'aikatan kiwon lafiya fiye da dubu 150. Kuma gaba daya ne an ceci wadanda suka jikata da fararen hula masu fama da bala'in fiye da dubu 380.

Ban da wannan kuma, a 'yan kwanakin nan da suka gabata, hukumomin kula da abinci na lardunan Hunan da Guizhou da Guangxi da ke fama da bala'in dusar kankara mafi tsanani sun dauki matakai iri daban daban domin ba da tabbaci ga kasuwannin samar da abinci na yankuna masu fama da bala'in mai tsanani, musamman ma yankunan da ke kan duwatsu kuma suke da wuyar zuwa.

Kuma an labarta cewa, ya zuwa yanzu, ana gudanar da kasuwannin samar da abinci na wurare daban daban masu fama da bala'in kamar yadda ya kamata, kuma an samu daidaituwa wajen farashin abinci.(Kande Gao)