Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-11 17:30:26    
An tabbatar da ayyukan da ya kamata a yi bayan bikin bazara a kasar Sin

cri

A ran 10 ga wata, cibiyar ba da umurni cikin gaggawa ta jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki da fama da bala'in dusar kankara ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya taro, inda ta tabbatar da ayyukan da ya kamata a yi bayan bikin bazara na kasar.

A gun wannan taro, an nuna cewa, za a kawo karshen hutun bikin bazara, yawan fasinjojin da za su koma guraban aikinsu daga garinsu zai kai matsayin koli nan gaba ba da dadewa ba. Aikin jigilarsu zai shiga hali mai tsanani. Sabo da haka, an nemi hukumomin da abin ya shafa da su kara mai da hankali kan sauyin yanayin duniya, kuma su tsara shirin fama da yanayi mai tsanani domin tabbatar da zirga-zirga. A waje daya kuma, dole ne a kara yawan jiragen kasa da na ruwa da motoci bisa yawan fasinjoji. Ya kamata wasu tasoshin jiragen kasa da na mota su kara wa dalibai da 'yan ci rani jiragen kasa da motoci. Bugu da kari kuma, dole ne a sanar wa jama'a sauyin yanayin duniya da halin da ake ciki a kan hanyoyin mota da na jiragen kasa cikin lokaci domin ba da jagoranci ga fasinjoji wajen zabar hanyoyin zirga-zirga da lokacin fita da magance tsayar da fasinjoji a tasoshin jiragen kasa da na mota.

Haka kuma, an nemi a tabbatar da jigilar kayayyakin masarufi zuwa yankuna masu fama da bala'in dusar kankara da sake gina wadannan yankuna. (Sanusi Chen)