Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-09 21:05:32    
An sake samar da wutar lantarki a wuraren da ke fama da bala'in dusar kankara

cri
Ya zuwa ran 9 ga wata da karfe 6 da yamma, kashi 94 bisa dari daga cikin yankunan kasar Sin da aka katse wutar lantarki sakamakon bala'in ruwa da dusar kankara sun sake samun wutar lantarki.

Wani jami'i na kamfanin tsarin wutar lantarki na kasar Sin ya bayyana cewa, lokacin da ake gamu da bala'in mafi tsanani, gidaje miliyan 22 ba su da wutar lantarki, amma yanzu gidaje fiye da miliyan 20 sun sake samun wutar lantarki, yawancin birane da gundumomin da ke fama da bala'in su ma sun sake samun wutar lantarki.

cibiyar ba da umurni cikin gaggawa ta jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki da fama da bala'in kankara mau laushi ta kasar Sin ta bayyana cewa, cibiyar ta riga ta daidaita muhimman shirye-shirye na haka da yin jigilar kwal da bukatun kwal da ake nema a watan Faburairu. Ya zuwa yanzu an riga an tabbatar da samar da kwal ga muhimman kamfanonin samar da wutar lantarki da makamashin kwal.(Kande Gao)