Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-08 21:03:21    
Hu Jintao ya gai da jama'ar jihar Guangxi

cri
Lokacin da ake murnar bikin bazara na gargajiya na kasar Sin, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya je birnin Nanning da shiyyar Baise na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gasashin kanta da ke kudancin kasar domin gai da 'yan kwadago da sojoji 'yan sanda wadanda suke cigaba da yin aiki a lokacin da ake murnar bikin bazara, kuma ya yi murnar bikin bazara da jama'ar al'ummomin jihar.

Tun daga ran 7 zuwa ran 8 ga wata, bi da bi ne Hu Jintao ya gai da sojoji 'yan sanda da 'yan kwadago da manoma, kuma ya wakilci kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ya taya murnar bikin bazara yana fatan jama'ar kabilu daban-daban za su samu fatan alheri da koshin lafiya a cikin sabuwar shekara.

Haka kuma, lokacin da Hu Jintao yake nuna wa 'yan kwadago na kamfanin kula da tsarin jigilar wutar lantarki na Guangxi, ya bayyana cewa, tabbatar da samar da wutar lantarki aiki ne mafi muhimmanci a cikin muhimman ayyukan fama da bala'in kankara mai laushi. Yana fatan za a iya yin gyara kan tsare-tsaren jigilar wutar lantarki cikin sauri. (Sanusi Chen)