
Yanzu, an riga an kawo karshen yanayin ruwan sama, da kankara mai laushi da kankara a kudancin kasar Sin. Ran 6 ga wata, hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta kasar Sin ta riga ta kawar da alamar gargadi kan bala'in yanayi.
Tun tskiyar watan Janairu, an yi ruwan sama da kankara mai laushi a wurare masu yawa da ke kudancin kasar Sin, kuma an sami bala'in yanayi mai tsanani. Saboda haka, hukumar kula da yanayin samaniya ta kasar Sin ta bayar da alamar gargadi kan bala'in yanayi tun daga ran 25 ga watan Janairu da ya gabata.
An ce, a cikin kwanaki 4 masu zuwa, za a samu kyakkyawan yanayi a kudancin kasar Sin, wannan ya dace da aikin raya zaman rayuwa da aikin kawo al'barka, da sufurin kayayyakin agaji.
|