Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 16:21:34    
Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa a bikin bazara

cri

Titin sayar da kayayyaki masu nuna sigogin musamman da za a bude a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan shi ma zai janyo hankulan mutane sosai, inda za a sayar da kayayyakin fasaha na gargajiya na kasar Sin da aka yi da hannu. Wasu kayayyakin wasa na yara masu dogon tarihi za su ba yara na yanzu mamaki kwarai, domin ba su ga taba ganin irinsu a da ba, sai a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin. A lokacin da suke halartar bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, masu yawon shakatawa za su sayi zane-zanen takarda da aka yanke da almakashi da takardun fatan alheri da aka manna su a kofa, ta haka za su koma gida tare da fatan alheri.

A gabashin birnin Beijing, a kan yi bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a gidan ibada na Dongyuemiao, shi ne daya daga cikin bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu dogon tarihi a Beijing. A bikin bazara na wannan shekara, za a yi bikin nune-nunen kayayyaki game da bera a gidan ibadar. Za a yi bayani kan al'adu dangane da alamar shekarar haihuwa ta bera ta hanyar nuna abubuwan al'umma kusan dari 1 tare kuma da hotuna da bayanai.

Masu sauraro, dazun nan na yi muku bayani kan bukukuwan wasannin kwaikwaiyo na gargajiya na kasar Sin da za a yi wurin yawon shakatawa na Ditan da gidan ibada na Dongyuemiao, su ne wasu biyu daga cikin dimbin bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da za a yi a nan Beijing a lokacin bikin bazara. A Beijing, za a yi irin bukukuwa gomai, wadanda suka nuna sigogin musamman nasu, suna kuma kushe da harkoki iri daban daban. A gun wadannan bukukuwa, za ku kara fahimtar al'adun gargajiya na mazauna Beijing, sa'an nan kuma, za ku kara fahimtarku kan yadda a kan yi murnar bikin bazara a sauren wurare na kasar Sin. A wurin yawon shakatawa na mutum-mutumi na Beijing a yammacin Beijing, za a shirya bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin game da al'adar bikin bazara a wannan shekara. Du Long, wanda ke kula da shirya wannan biki, ya gaya mana cewa, Babban taken bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da za mu yi shi ne al'adar bikin bazara na kasar Sin. Za mu nuna sigogin musamman game da yadda kabilu daban daban na kasar Sin su kan yi murnar bikin bazara ta hanyoyi daban daban a wurare daban daban. Yanzu mun tsara wasannin kwaikwayo iri daban daban game da yadda mazauna lardunan Shanxi da Hubei da Yunnan da Guizhou da kuma Guangdong suka yi bikin bazara. Wadannan larduna 5 su ne wakilai na yankuna na gabas da kudu da yamma da arewa da kuma tsakiya na kasar Sin a fannin yin bikin bazara ta hanyoyi daban daban. Sa'an nan kuma, za ku iya dandana ko kuma kallon abinci da kayayyakin da shahararrun tsoffin shagunan sayar da abinci gomai da kwararrun kananan sana'o'i za su kawo muku.'

Saboda Beijing ta kara bude kofarta ga kasashen duniya, baya ga ci gaba da bin al'adun gargajiya, ta kuma hada wasu abubuwan zamani a cikin bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin. A wurin yawon shakatawa na Shijingshan da ke yammacin Beijing, a ko wace shekara a kan yi bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin mai nuna sigar musamman ta kasashen duniya. Wu Hailong, mai kula da wannan wurin yawon shakatawa, ya yi karin bayani cewa,'Bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da za mu yi zai hada da kallon gine-gine na salon kasashen Turai da kallon wasannin kwaikwayo masu sigogin musamman na kasa da kasa da kuma dandana abinci daban daban na kasashen waje. Muna fatan bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da za mu yi zai samar wa kasashen duniya wani dandamalin nuna sigogin musamman na al'adunsu da na aikin yawon shakatawa.'

Kazalika kuma, irin wadannan bukukuwa su kan samar da kyakkyawan yanayi a Beijing a lokacin bikin bazara. Jiang Lingling, wani dalibi da yake karatu a Beijing, tare da iyayensa ya kan halarci irin wadannan bukukuwa a lokacin bikin bazara a ko wace shekara. Ya ce, 'A ganina, bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin na cike da annashuwa, na kan ci abinci mai dogon tarihi na Beijing, ban da wannan kuma, na kan sayi kayayyakin fasaha na al'umma.'


1 2