Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-04 21:29:49    
Larduna 7 na kudancin kasar Sin sun sake samun kudaden agaji Yuan miliyan 700 da ma'aikatar kudi ta samar

cri

A ran 4 ga wata, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta sake samar da kudin Sin wato Yuan miliyan 700 ga lardunan Hunan da Guizhou da Jiangxi da dai sauran larduna hudu da ke fama da bala'un sanyi da ruwan kankara da kuma dusar kankara masu tsanani domin tallafa wa jama'a masu fama da bala'in da shawo kan cututtuka da samar da kayayyaki da kuma sake farfado da ayyukan samarwa da kuma zaman jama'a.

Haka kuma a ranar, ma'aikatar kudi da kuma ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin sun kebe kudin taimako Yuan miliyan 710 domin samar da kudin alawus na watanni uku ga fararen hula da ke zaman rayuwa mafi kankanta na birane da kauyukan da ke cikin wadannan larduna 7 da ke fama da bala'in.

Bugu da kari kuma, ma'aikatun kudi da aikin gona na kasar sun sake kebe kudin taimako Yuan miliyan 40 domin taimaka wa lardunan Zhejiang da Guangdong da Yunnan da Shanxi da dai sauran larduna uku da ke fama da bala'in mai tsanani wajen farfado da ayyukan samar da amfanin gona.

A ran nan kuma, kudade da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan dubu 650 da kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta tattara sun riga sun isa birnin Chengzhou na lardin Hunan da ke fama da bala'in mafi tsanani.

Ya zuwa ran 4 ga wata da karfe 2 da yamma, kungiyar agaji ta Red Cross ta riga ta samu kudi da kuma kayayyakin da darajarsu ya kai fiye da Yuan miliyan 31 da zaman al'umma ke samarwa.(Kande Gao)