Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-01 21:36:38    
Kasar Sin na tinkarar bala'un ruwan sama da dusar kankara cikin himma

cri

A kwanan baya, larduna fiye da 10 a yankunan tsakiya da gabas da kudu na kasar Sin sun gamu da munanan bala'un ruwan sama da dusar kankara, wadanda ba su gamu da irinsu a shekaru gomai ba. Bala'un sun kawo babbar illa ga kasar Sin a fannonin sufuri da zirga-zirga da samar da makamashi, haka kuma, sun kawo wa mutane wahalhalu a fannonin zaman rayuwa da aikin kawo albarka. Yanzu bala'un na ci gaba da shafar kasar Sin. A wurare daban daban na kasar Sin mutane suna tinkarar munanan bala'un cikin himma domin namijin kokari wajen rage illar da bala'un ke kawo musu, da kuma tabbatar da samar da isassun kayayyakin masarufi a wuraren da ke fama da bala'un.

A ran 1 ga wata, Zou Ming, mataimakin shugaban sashen harkokin ba da agaji na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, bala'un ruwan sama da dusar kankara da ake fuskanta a yanzu sun kawo wa wurare da yawa babbar illa har na dogon lokaci, sun kuma yi babbar hasara da ba a taba ganin irinta a da ba. Yanzu ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta kaddamar da shirin ko-ta-kwana na ba da agaji a sakamakon bala'i daga indallahi domin bai wa masu fama da bala'un taimako. Ya ce,'Ya zuwa yanzu dai, baitulmalin tsakiya na kasar ya riga ya ware kudin ba da agaji mai yawan yuan miliyan 431, sa'an nan kuma, hukumomin lardunan da ke fama da bala'un sun kebe kudade da kayayyaki da yawa. Ban da wannan kuma, ma'aikatarmu ta yi jigilar tufafin sanyi da barguna cikin gaggawa, yanzu ana rarraba su misalin kashi 70 cikin kashi dari zuwa masu fama da bala'un. Abun da za mu yi a mataki na gaba shi ne za mu mai da hankali sosai kan sauye-sauyen bala'un, za mu kaddamar da shirin ko-ta-kwana cikin lokaci da rarraba ayyuka, a sa'i daya kuma, za mu rarraba ayyuka da share fagen sake gina wuraren da ke fama da bala'un.'

An yi karin bayani cewa, kayayyakin ba da agaji da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta tura a rukuni na farko sun isa wuraren da suka fi fama da bala'un.

Matsalar karancin makamashi na daya daga cikin munanan illolin da bala'in dusar kankara ke kawowa. Ran 31 ga watan jiya, lokacin da yake rangadin aiki a lardin Shanxi, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya nuna cewa,'A halin yanzu, yawancin wurare da ke kudancin kasarmu na fuskantar munanan bala'un ruwan sama da dusar kankara. Mazauna wuraren suna shan wahala sosai a zaman rayuwa da aikin kawo albarka. Yanzu wadannan wurare na matukar bukatar kwal, ta haka za a samar da wutar lantarki. Masu fama da bala'un ba za su maido da aikin kawo albarka da zaman rayuwarsu ba sai an samar da wutar lantarki. Ina fatan tare da sharadi na farko, wato a cikin yanayin kwanciyar hankali ne za a samar da karin kwal domin sassauta matsalar karancin kwal a yanzu, ta haka, za a tabbatar da gudanar da harkokin tattalin arziki da zaman al'ummar kasa a kasar China.'

Mummunan yanayi na tsawon kwanaki da dama ya kuma kawo mugun illa kan hanyoyin dogo da hanyoyin mota da jiragen sama masu daukar fasinja a kasar China, an tsayar da jiragen kasa da yawa, kuma an dakatar da su, ko kuma an daina ayyukansu, musamman ma a kudancin kasar.

Malama Wei Rengui ta yi aiki a birnin Guangzhou daga garinta na birnin Wuhan, ta yi shirin komawa gida a lokacin bikin bazara, amma an tsayar da ita a tashar jiragen kasa ta Guangzhou domin mummunan yanayi. Ta ce,'Na yi shirin komawa gida a lokacin bikin bazara, amma saboda mummunan yanayi, na ci tura, na ji bakin ciki. Duk da haka, shugabannin Guangzhou a matakai daban daban da wadanda abin ya shafa sun kula da mu sosai, sun ba mu abinci da wuraren kwana, mun ji sauki a zukatanmu.'

Don tabbatar da ganin malama Wei Rengui da sauran fasinjoji kamar ita za su koma gida, hukumomin zirga-zirga ta kasar Sin da abin ya shafa suna yin dabara domin tabbatar da sufuri da zirga-zirga yadda ya kamata.

Yanzu ma'aikatar gudanarwa ta kasar Sin ta kafa cibiyar jagorantar yaki da bala'in dusar kankara domin sassauta matsalar karancin kwal da man fetur da kuma matsalar sufuri da zirga-zirga. (Tasallah)