Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-01 21:34:53    
Gwamnatin kasar Sin tana matukar kokarin fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara

cri

A ran 1 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya shugabanci taron majalisar gudanarwa, wato gwamnatin kasar, inda aka yi nazarin fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara da tabbatar da zirga-zirga da sufurin kayayyaki.

A cikin kwanaki da dama da suka gabata, an samu bala'in ruwan sama da dusar kankara da ruwan sanyi da ba a taba ganin irinsu a cikin dimbin shekarun da suka gabata ba a wasu yankunan kasar Sin. Wannan bala'i ya kawo babbar illa ga ayyukan zirga-zirga da na sufurin kayayyaki da aikin samar da makamashi a kasar. Kuma bisa labarin da hukumar kula da yanayi ta kasar Sin ta bayar, an ce, a cikin wasu kwanaki masu zuwa, za a ci gaba da yin ruwan sama da dusar kankara da ruwan sanyi a yawancin yankunan kudancin kasar Sin, wato wannan bala'i zai tsananta.

Salibi da haka, gwamnatin kasar Sin ta nemi hukumomin wurare daban-daban na kasar da su tsara hakikanan matakai domin tabbatar da ganin an samu zirga-zirgar hanyoyin mota da hanyoyin dogo da samar da wutar lantarki a yawancin wurare da tabbatar da farashin kayayyaki a kasuwa kamar yadda ya kamata kafin bikin bazara, wato bikin gargajiya mafi muhimmanci a kasar Sin. A waje daya kuma, ta nemi a tsugunar da fasinjoji da fararen hula wadanda suke fama da bala'in.

Bayan wannan taro, ba tare da bata kowane lokaci ba ne, firayin minista Wen Jiabao ya sake zuwa lardin Hunan inda ake fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara sosai domin rangadin aikin fama da wannan bala'i. Bugu da kari kuma, tun daga ran 28 zuwa ran 30 ga watan Janairu, sauran manyan jami'an kasar Sin bi da bi ne suka yi rangadin aiki a yankunan da suke fama da bala'i domin nuna jaje ga jama'a masu fama da bala'in.

An labarta cewa, mutane 60 sun mutu sakamakon bala'in ruwan sama da dusar kankara da yake faruwa a wasu yankunan kudancin kasar Sin. Wannan bala'i ya haddasa hasarar tattalin arzikin kudin Sin yuan biliyan 54. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta riga ta kebe kudin Renminbi yuan miliyan 431 daga baitulmali na gwamnatin tsakiya domin fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara.

Haka kuma, bisa umurnin da shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar Mr. Hu Jintao ya bayar, yawan sojojin da aka aika da su zuwa yankuna masu fama da bala'i ya riga ya kai dubu 250 tare da sojojin farar hula dubu 770. Sannan kuma, a kwanann baya, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta kafa wata cibiyar ba da jagoranci kan aikin sufurin kwal da wutar lantarki da man fetur da fama da bala'u daga indallahi cikin gaggawa. (Sanusi Chen)