Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-01 20:10:48    
An kafa cibiyar ba da jagoranci kan aikin sufurin kwal da wutar lantarki da man fetur da fama da bala'u daga indallahi cikin gaggawa a kasar Sin

cri
A kwanann baya, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta kafa wata cibiyar ba da jagoranci kan aikin sufurin kwal da wutar lantarki da man fetur da fama da bala'u daga indallahi cikin gaggawa domin kara karfin ba da jagoranci kan aikin warware manyan batutuwan da ke shafar ayyukan sufurin kwal da wutar lantarki da man fetur da bala'u daga indallahi.

Hukumomi 23 gwamnatin kasar Sin, ciki har da kwamitin yin gyare-gyare da neman cigaban kasar Sin da ma'aikatar kula da harkokin jama'a da ma'aikatar hanyar dogo ta kasar su ne mambobin wannan cibiyar. Babban nauyin da ke bisa wuyan wannan cibiya shi ne sanin halin da ake ciki a kan wadannan ayyuka da daidaita su a tsakanin ma'aikata daban-daban da sana'o'i daban dabam da kuma yankuna daban-dabam.

An labarta cewa, mutane 60 sun mutu sakamakon bala'in ruwan sama da dusar kankara da yake faruwa a wasu yankunan kudancin kasar Sin. Wannan bala'i ya haddasa hasarar tattalin arzikin kudin Sin yuan biliyan 54. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta riga ta soma aiwatar da shirin fama da bala'u daga indallahi cikin gaggawa. Bisa wannan shiri, an riga an kebe kudin Renminbi yuan miliyan 431 daga baitulmali na gwamnatin tsakiya domin fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara. A waje daya kuma, an riga an isar da kayayyakin jin kai a karo na farko a lardunan Guizhou da Guangxi da suke cikin hali mafi tsanani wajen fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara. (Sanusi Chen)