Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-30 18:44:45    
Kasar Sin tana rubanya kokari wajen tabbatar da zirga-zirga cikin kwanciyar hankali

cri

Saurari

Yanzu larduna da birane fiye da 10 na yankin tsakiya da na gabas da na kudancin kasar Sin suna shan wahalar ruwan sama kamar da bakin kwarya da mugun bala'in kankara mai laushi, wadanda ba a taba ganin irinsu a shekaru gomai da suka wuce ba. Mummunan yanayin ya kawo wa kasar Sin illa ta fuskar hanyoyin dogo da hanyoyin mota da jiragen sama masu daukar fasinjoji sosai. A kwanan baya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayim minista Wen Jiabao na kasar da sauran kusoshin kasar sun bukaci hukumomin gwamnatin a matakai daban daban da su yi dabara domin tabbatar da zirga-zirga yadda ya kamata da kuma samar da isasshen wutar lantarki, kuma su dauki matakan a-zo-a-gani domin mayar da moriyar fararen hula a gaba da kome.

Irin wannan mummunan yanayi ya zo ne kafin bikin baraza na gargajiya na kasar Sin, wanda ya fi muhimmanci ga Sinawa, kuma lokaci ne da dimbin mutane suke alla-alla wajen komawa garinsu domin murnar bikin bazara tare da iyalansu. Shi ya sa aka fi fuskantar matsaloli wajen zirga-zirga da sufuri, musamman ma hanyoyin sufuri na daukar fasinjoji.

Ga misali, a bangaren hanyar dogo a tsakanin biranen Beijing da Guangzhou da ke birnin Changsha na lardin Hunan, yanzu an dakatar da jiragen kasa masu daukar fasinjoji fiye da 30, kuma an tsayar da yawancin fasinjojin a tashar jiragen kasa ta Changsha.

Ran 29 ga wata, cikin halin aminci firayim minista Wen Jiabao ya gana da fasinjojin da ke cikin tashar jiragen kasa, ya kuma nuna musu jinjina. Ya ce,'Ina neman gafara daga wajenku domin an tsayar da ku a nan. Muna gaggauta yin gyara. Da farko dai, muna gaggauta gyara tsarin ba da wutar lantarki. Jiragen kasa za su yi aiki bayan da tsarin ba da wutar lantarki ya fara aiki. Ba ku bukatar dogon lokaci, domin kowa da kowa zai koma gida domin bikin bazara. Bikin bazara tana kan hanya, ina taya muku murnar bikin bazara tukuna. Na gode.'

Yanzu hukumomin kula da hanyoyin dogo na kasar Sin suna gaggauta ayyukansu domin neman maido da odar sufuri a hanyar dogo a tsakanin Beijing da Guangzhou cikin sauri.

A lokacin da suke fuskantar matsalolin da bala'in kankara mai laushi ke kawowa, fasinjoji sun nuna fahimtarsu. Malam Gou Ming, wani fasinja da aka tsayar da shi a tashar jiragen kasa ta Guangzhou ya ce,'Na taba jin damuwa, amma daga baya na kwantar da hankali kadan. A ran 26 ga wata, na iso tashar jiragen kasa ta Guangzhou daga birnin Shenzhen, ina ta jiran jirgin kasa domin komawa gida. Iyalina sun sha bugo mini wayar tarho da matsa mini komawa gida saboda bala'in kankara mai laushi. Na rasa abin da zan yi. Amma abin farin ciki shi ne hukumar Guangzhou ta ba mu abinci a fayu, ta kuma ba mu wurin kwana. Ina mata godiya. A gaskiya, na sayi tikiti, zan shiga jirgin kasa, wajibi ne in kula da wadannan abubuwa da kaina. Amma gwamnatinmu ta ba mu wadannan abubuwa a fayu. Muna mata godiya sosai. Ko da yake ana sanyi sosai, amma ba na jin sanyi a zuciyata.'

Hanyoyin mota kuwa, ruwan sama na kankara na tsawon kwanaki da dama ya sanya fuskokin hanyoyin mota sun daskare, ta haka, an sami cunkuson motoci a kan hanyoyin mota kwarai. Babbar hanya a tsakanin Beijing da Zhuhai ta fi fuskantar cunkuson motoci. Amma yanzu, hukumomi na matakai daban daban na wuraren da babbar hanya a tsakanin Beijing da Zhuhai ta ratsa suna bai wa fasinjoji da ma'aikatan motoci da suka sami tsaiko abinci da ruwan sha da barguna, sun kuma kai wa tsoffi da yara a sauran wurare. Hukumar lardin Hunan ta aika da sojoji kusan dubu 200 domin ba da agaji cikin gaggawa.

Zhang Chunxian, sakataren kwamitin lardin Hunan na jama'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya jagoranci ayyukan yaki da bala'i kai tsaye, ya bayyana cewa, muhimmin aiki da za a yi cikin gaggauwa shi ne a kwashe wadanda suka sami tsaiko. Ya ce,'Kwashe su cikin manyan motoci zai yi kyau, amma in babu manyan motoci, to, kananan motoci za su yi. Za mu kwashe fararen hula zuwa birninmu a cikin kananan motoci. Za mu yi amfani da makarantu da asibitoci da otel-otel domin tsugunar da su, za mu ba su abinci da abin sha a fayu.'

Kazalika kuma, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin da ma'aikatar kudi ta kasar Sin sun zuba wa lardunan Hubei da Hunan da sauran wurare na tsakiyar kasar kudin Sin fiye da miliyan 1 domin kwashewa da sake tsugunar da fararen hula masu fama da bala'i, da kuma tabbatar da sufurin cikin kwanciyar hankali.(Tasallah)