 A ran 28 ga wata da dare, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya tafi lardin Hunan daga birnin Beijing, don duba aikin yaki da bala'in kankara.
Sabo da an rufe filin jirgin sama da ke birnin Changsha na lardin Hunan, firaminista Wen Jiabao ya sauka a filin jirgin sama na Tianhe na lardin Hubei, daga baya kuma, ya kai birnin Changsha a ran 29 ga wata da sassafe ta hanyar jirgin kasa, sai ya fara yin tattaunawa da jami'an hukumomi da abin ya shafa da gwamnatin lardin Hunan kan yadda ake yaki da bala'in kankara da ba da agaji nan da nan.
Tun daga ran 13 ga watan Janairu, lardin Hunan na kasar Sin ya shiga lokacin karawar sanyi mafi tsanani tun da aka shiga lokacin sanyi, a samu bala'in kankara mafi tsanani da ba a taba ganinsa ba cikin shekaru sama da 50 da suka wuce. Bala'in nan ya shafi wurare masu yawa sosai, kuma an yi ta yinsa cikin dogon lakaci, ana shan wahalar bala'in nan sosai. (Zubairu)
|