Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-10 21:58:19    
Kogunan dutsen Xumi na jihar Ningxia

cri

Kogunan dutsen Xumi yana arewa maso yammacin birnin Guyuan da ke kudancin jihar Ningxia. Kuma ma'anar Xumi ita ce dutsen da ke da dukiyoyi. An iya samun duwatsu iri daban daban a dutsen Xumi, kuma idan lokacin zafi da lokacin kaka yayi, ana iya samun bishiyoyi masu launin kore da 'ya'yan itatuwa a ko ina a kan dutsen, shi ya sa yana da kyan gani sosai.

Dutsen Xumi kyakkyawan wurin shan iska ne da ba safai a kan iya gani a kan Plateaun Huangtu da ke arewa maso yammacin kasar Sin ba. Ban da wannan kuma dutsen yana taka muhimmiyar rawa a fannin fasaha. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ake iya samun manyan koguna a kan dutsen wadanda aka yi a daulolin Beichao da Sui da kuma Tang. Shi ya sa wurin ya zama wani muhimmin kayan tarihi na al'adun gargajiya na kasar Sin, kamar kogunan dutse na Dunhuang da na Yungang da na Longmen na kasar.

Hoton Sakyamuni da aka yi a kan dutse a daular Tang wato a shekara ta 849 hoton dutse ne mafi girma a cikin kogunan dutsen Xumi, wanda tsayinsa ya kai mita 26.

Kogunan dutsen Xumi ya bayyana fasahohin sassaka abubuwan addinin Buddhism a kan duwatsu daga tsakiyar daular Beichao zuwa daulolin Sui da Tang, kuma su ne kayayyakin tarihi na al'adu masu daraja da ke kan hanyar siliki, da kuma abin shaida ne na tarihi wajen yin cudanyar tattalin arziki da al'adu tsakanin Sin da kasashen waje.