Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 10:43:49    
Wani shahararren tauraron dan wasan sinima na kasar Sin mai suna Li Lianjie

cri

Li Lianjie mai shekaru 44 da haihuwa shi ne wani dan wasan sinima da ya yi suna sosai a kasashen duniya. A shekarar 1982, ya soma nuna wasan Gongfu a karo na farko a cikin sinimar da ke da lakabi haka: Temple Shaolin, ya zuwa yanzu, ya riga ya nuna wasan Gongfu a cikin sinima da yawansu ya kai 33. A kwanan baya ba da dadewa ba, a birnin Beijing, an soma nuna sinima mai suna "Huo Yuanja" wanda Mr Li Lianjie ya zama babban dan wasa a ciki. A cikin sinimar, an bayyana cewa, a karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20, an sami wani labari dangane da duk zaman rayuwar Huo Yuanjia wanda ya kasance kakan tsohon hannu na wasan Gongfu.

A lokacin da Mr Li Lianjie yake karami, an kira shi da cewar wai yaro mai kwarewar wasan Gungfu . Lokacin da ya shiga aji na biyu a makarantar firamare, ya nuna fiffikonsa sosai wajen nuna wasan Gongfu a kos din horar da fasahar wasan Gonfu, sai an shigar da shi cikin kungiyar nuna wasannin Gongfu ta Beijing don ya zama wani dan wasan Gongfu . Sa'anan kuma, Li Lianjie ya yi kokarin koyon fasahar wasan Gongfu , ya zama dan wasan Gongfu a hukunce, daga bisani kuma, ya zama shahararren dan wasan Gongfu na sinima. Mr Li Liangjie ya bayyana cewa, a wancan lokaci, ban sa ran alheri sosai ga makomata a nan gaba ba, sai na yi tsammani cewa, kamata ya yi na sami kudi da yawa don rage nauyin da ke bisa wuyan mahaifiyata, da kuma bari mahaifiyata ta kwantar da hankalinta ba tare da damuwar da ta yi a kan abubuwan da na yi ba, kuma mahaifiyata ta yi alfahari da samun danta kamar ni kaina na ke yi, duk saboda na riga na rasa mahaifina.

Bisa matsayin dan wasan Gongfu, Mr Li Lianjie ya zama zakara sau da yawa a cikin gasar wasan Gongfu da aka shirya, kuma ya kai ziyara a kasashe fiye da 40. A shekarar 1982, Zhang Xinyan ,babban direktan wasan sinima mai suna "Temple Shaolin" ya zabi Mr Li Lianjie da ke da shekaru 17 da haihuwa don ya zama babban dan wasa, a cikin sinimar, ya zama wani sufi mai bin addinin Bhudah na Temple Shaolin da ke kwarewar Gongfu sosai kuma na da halin nuna adalci sosai. Bayan da aka nuna sinimar, sai mutane sun burge sosai da sosai, kuma sinimar ta zama wani babbar alamar da ke cikin zaman rayuwar Li Lianjie.

Amma, bayan da Li Lianjie ya kammala aikin daukar sinimar, sai ya shiga lokacin fama da wahaloli masu tsanani sosai, duk saboda ya fadi kuma ya karya kwaurinsa a cikin wani horon da aka yi masa, Mr Li Lianjie ya bayyana cewa, an yi mini aikin tiyata cikin sa'o'i 7, wannan ne babban bugun tsiya da aka yi mini , likita ya ce, ya iya ba da alkawari gare ni cewar wai zan iya tafiya, amma ba zan iya ci gaba da wasan Gonfu ba. Saboda haka a cikin watanni biyun da na ke kwantawa a cikin asibiti, sai na yi kuka sau da yawa har da hawaye, ban san yadda zan yi a nan gaba ba, a wancan lokaci, kamfanin sinima ya ce, bai kamata ba a tono labarin nan, amma ni kaina ina soma damuwa da makomata ta nan gaba.

Bayan wannan, Mr Li Lianjie ya ga tilashi ne ya daina zaman rayuwarsa na yin wasan motsa jiki, kuma ya shiga rukunin daukar wasan sinima, wato ya tafi Hongkong don daukar sinima dangane da wasan Gongfu .

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, Yawan sinimar da Li Lianjie ya dauka ya wuce goma ko fiye, sa'anan kuma Li Lianjie ya kaura zuwa kasar Amurka, ya sami sabon ci gaba wajen daukar sinima. Bi da bi ne ya dauki sinimar da ke da lakabi " Lethal Weapon 4" da sinimar "Romeo Must Die" da sinimar "Kiss of the Dragon" da sauransu.

Kodayake Mr Li Lianjie ya sami aiki a Holliwood na kasar Amurka, anna yana ci gaba da kasancewa cikin halinsa na tsayawa tsayin daka bisa gargajiyar kasar Sin, ya bayyana cewa, a gaskiya dai mutane da yawa suna yi mini kauna sosai, kuma sun mayar da ni tamkar yadda wata alamar nuna bajinta a cikin zuciyarsu, amma duniyata tana babbar nahiyar Asiya, kodayake ka je wani gefe daban na duniya, amma sai mutanen da suke kaunar sinimar kasar Sin, ko wadanda suke kaunar sinimar nuna wasan Gongfu da Hongkong ya dauka suka fahimtarka kawai, kuma a kan hanyar da kake wucewa, ba wanda ya san ka, saboda haka, na gane sosai cewa, dole ne zan soma daga sifiri.

A shekarar 2007, Li Lianjie ya kafa wani asusu tare da kungiyar Red Cross ta kasar Sin, yana son ya yi kokarin samar da taimako ga wadanda suke fama da masifa a cikin mawuyacin hali.(Halima)