Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-25 15:42:43    
Kolejin Confucius ya ba da sauki ga kasashen ketare wajen koyon Sinanci

cri

Kwanan baya, an kafa kolejin Confucius ta farko ta rediyo a hukunce a gidan rediyon kasar Sin, wato CRI. Wannan ne labari mai kyau ga abokanmu na kasashen ketare, wadanda ke sha'awar koyon Sinanci, da kuma al'adun kasar Sin, saboda an kara gabatar da wata sabuwar hanyar koyon Sinanci. Nan gaba kuma, masu sauraronmu da ke kasashen waje za su iya koyon Sinanci da sauki wato ta hanyar sauraran shirye-shiryen da kolejin watsa labarai ta Confucius ta bayar ko kuma karanta shafuffukan Internet na wannan koleji.

Masu sauraro, abin da kuke saurara a yanzu shi ne, wata yarinyar kasar Serbia ce da ke da shekaru 19 na haihuwa na karanta littafi da Sinanci na gargajiya. Wannan yariniya tana da wani suna na Sinanci mai dadin ji, wato Su Lina. Nan da shekaru uku da suka wuce, ta zo kasar Sin ne tare da mamarta, wanda ke yin aiki a nan kasar Sin. Mamarta Su Chunyu ta gaya mana mana cewa,

"A farkon watanni uku bayan da Su Lina ta isa kasar Sin, ba ta iya magana da Sinanci ko kadan. Amm, daga baya kuma, a lokacin da take gamuwa da matsaloli wajen harshe, ta kan tambaye ni, yanzu shekaru uku su wuce, ta riga ta iya Sinanci sosai."

Lallai dalilin da ya sa Su Lina ta iya Sinanci cikin sauri shi ne, tana koyon wannan sabon harshe cikin muhalli na yarensu na kansu. An kafa kolejin Confucius kan rediyon ne bisa wannan ra'ayin koyarwa. Bisa labarin da muka samu an ce, gidan rediyon kasar Sin wato CRI da kuma babban zauren koleji Confucius su ne suka kafa wannan koleji kafada da kafada, inda za a kaddamar da jerin shirye-shirye kan koyarwa cikin harsunan waje 38 duk bisa littattan karatu bai daya kan harshen Sinanci. Za a watsa wadannan shirye-shirye ne ga yankuna daban-daban na duniya ta rediyo da kuma hanyar sadarwa ta internet da dai sauransu.


1 2