Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-19 21:46:42    
Makarantar koyar da harshen Larabci ta Yuhai da ke gundumar Tongxin

cri

Makarantar koyar da Larabci ta Yuhai tana daya daga cikin makarantun koyar da harshen Larabci na gundumar Tongxin da ke kudancin jihar Ningxia, wadda aka kafa ta a shekarar da ta gabata.

Shugaban makarantar Hei Xinmin ya gaya mana cewa, dimbin gidaje na wurin suna fama da talauci sosai, ba su da abinci, har ma ba su da ruwan sha. Amma idan suna son fitar da kansu daga talauci, dole ne a samu ilmi da fasaha. Ganin haka, iyaye masu yawa sun tsai da kudurin tura yaransu cikin makarantun koyar da Larabci. Ta haka za su iya samun kudade da yawa, kuma za su canja zaman rayuwarsu kwata kwata.

Li Xiaohu wani dalibi ne da ke cikin makarantar, kuma ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa ya zo makarantar shi ne sabo da yanzu Sin da kasashen Larabawa suna ta kara yin cudanya tsakaninsu, ana bukatar masu aikin fassara da Larabci da yawa, shi ya sa ya zo makarantar domin koyon harshen, daga baya kuma zai iya zuwa birane masu ci gaba na kasar Sin domin cin rani.

Ban da harshen Larabci, makarantar ta koyar da ilmin cinikayya da na Kwamfuta da na Turanci, ta yadda dalibai za su iya cancantar ayyukansu cikin sauri bayan da suka gama karantunsu daga makarantar.

Ya zuwa yanzu, dalibai fiye da 1000 sun riga sun gama karantunsu daga makarantar, kuma 700 daga cikinsu suna gudanar da aikin fassara a biranen Guangzhou da Yiwu da Shenzhen da dai sauran biranen kasar Sin.