Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-12 18:36:17    
Masallacin Tongxin na jihar Ningxia

cri

Masallacin Tongxin na jihar Ningxia yana kan wani tudun da ke arewa maso yammacin tsohon gundumar Tongxin. Kuma an ce an kafa shi a daular Ming wato tsakanin shekara ta 1573 zuwa 1619, sabo da haka masallacin yana daya daga cikin masallatai mafi girma da ke da dogon tarihi na jihar Ningxia.

Sifar masallacin Tongxi tana shan bamban da sauran masallatai na kasar Sin, ya yi kama da wata fada. An gina wannan masallaci a kan wani tudun da tsayinsa ya kai mita 10 kuma fadinsa ya kai murabba'in mita 3500. gine-gine mafi muhimmanci na masallacin su ne babban dakin yin salla da kuma Mi'dhanah, inda musulmai kusan 1000 suke iya yin salla tare.

Haka kuma masallacin ya hada sigar timba ta gargajiya ta kasar Sin da fasahohin sassakar itace na musulunci tare, shi ya sa ana iya ganin cewa, irin wannan salon gine-gine na musamman shi ne sakamako mai kyau wajen yin zama cikin lumana da yin cudanyar al'adu tsakanin kabilu daban daban na kasar Sin da ke jihar Ningxia.

Ban da wannan kuma babban masallacin Tongxin yana da nasaba da juyin juya hali na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Lokacin da jajayen sojoji na kasar Sin ke yin yaki a yammacin kasar a shekara ta 1936, an taba kafa gwamnatin Yuhai ta kabilar Hui mai cin gashin kai, haka kuma wannan shi ne karo na farko da 'yan kabilar Hui suka iya tafiyar da harkoki da kansu.(Kande)