Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-11 16:09:18    
Likita Fei Long a fannin likitancin kasar Sin daga Afrika

cri
Likita Fei Long ya zo kasar Sin ne daga kasar Cameroon, don koyon likitancin gargajiya na kasar Sin. A shekaru hudu da suka wuce, gwamnatin kasar Cameroon ta aika da shi zuwa kolejin likitancin gargajiya ta kasar Sin ta jihar Shanxi, domin neman digirin warkar da ciwon hanyoyin jigilar kuzari ta yara, bayan haka kuma, yana aiki bisa son ransa a asibitin warkewar ciwon rashin laka da kuzari ta yara ta jihar Shanxi har zuwa yanzu. Fei Long da ke da shekaru 32 na haihuwa ya kan gabatar da sunansa ga saura cewa, kalmar "Fei" na nuna Afrika, kalmar "Long" wato "Dragon" na kasar Sin. Ya gaya wa wakilinmu cewa, ya taba koyon ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin a Cameroon,

"A lokacin da nake karatu a jami'ar likitanci a kasar Cameroon, na soma nuna sha'awa kan wasu dabarun jiyya na halitta, a gani na likitancin gargajiyar kasar Sin na ci gaba a wannan fani. Akufanca ta likitancin kasar Sin na da amfani sosai."

A lokacin da wakilinmu ke yin ziyara a asibitin warkewar ciwon rashin laka da kuzari ta yara ta jihar Shanxi, likita Fei Long yana yin tausa ga wani yaro da ke da shekaru 15 na haihuwa.

Madam Guo Zhixin, shugabar asibitin ta gaya wa wakilinmu cewa: "Likita Fei Long yana yin tausa sannu sannu, saboda haka, yara suna son samun jiyya daga Fei Long."

Likita Fei Long ya ce: "Ina kaunar yara sosai, ba zan dakatar da aikina saboda wai na gaji ba, tila ne na yi iyakacin kokari domin yin jiyya ga wadannan yara."

Wadannan yaran da suke kamu da ciwon ciwon rashin laka da kuzari, yawancinsu suna rashin lafiya a fannonin hankali, da kuma yiwuwar motsa jiki, saboda haka, ana bukatar dogon lokaci da kuma hakuri wajen aikin jiyya. Likita Shi Xiaojie da ke yin aiki tare da Fei Long ya nuna yabo sosai ga Fei Long, ya ce,

"Ya fi mu mai da hankali kan aiki, yana kaunar yara sosai, kuma yana kaunar wannan aiki."

A lokacin hutu kuma, likita Feilong ya kan yi ciniki a tsakanin kasashen waje da Sin. Abokansa su kan samu takardun oda daga kasar Cameroon, ko sauran kasashe, daga baya kuma, Fei Long ya sayi kayayyaki daga kamfannonin kasar Sin, wadanda ke hade da abubuwan kyauta, da kayayyakin likitanci, da kuma wasu kayayyakin lantarki, da dai sauransu. Ya ce, yanzu kasar Sin na iya kera kusan dukkan kayayyaki, kuma wadannan kayayyaki na da inganci sosai, saboda haka, mutane da yawa suna son su sayi kayayyakinsa.

Likita Fei Long ya riga yana dacewa da zaman rayuwar jama'ar wurin, ya ji kamar shi wani mutum ne na jihar Shanxi. Lallai zaman rayuwarsa a kasar Sin har shekaru hudu ya kawo tasiri sosai gare shi. Yana fata zai zama a kasar Sin har abada,

"Ina jin farin ciki sosai saboda na iya zama da kuma aiki a kasar Sin, ina son jihar Shanxi, ina son kasar Sin, kuma ina fata zan kafa gida a nan, na riga na mai da kasar Sin kasata ta biyu."

Fei Long ya gayawa wakilinmu cewa, yana son abincin alkama, kuma yana iya magana da yaren wurin, a lokacin hutu yana son wasan Kongfu, yana nuna fatan alheri ga kasar Sin daga zuciyarsa.