Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-06 16:40:08    
Wurin shan iska na Shapotou

cri

Yau na je wurin shan iska na Shapotou don yin ziyara. Wurin shan iska na Shapotou yana bakin hamadar Tengger wanda yake da kilomita 20 da yammacin birnin Zhongwei na jihar Ningxia, inda ake iya samun hamada da rawayan kogi da duwatsu da zanguna tare, kuma a wurin, ana iya ganin kyan karkara na arewa maso yammacin kasar Sin da kuma na kudacin kasar gaba daya. Haka kuma sabo da wurin yana da halin musamman sosai, shi ya sa kwararru wajen yawon shakatawa sun nuna yabo sosai gare shi, kuma suna ganin cewa, wannan wani wurin shan iska na hamada ne daya tak a duk duniya.

A cikin wurin shan iska na Shapotou, akwai wata gangarar hamada da tsayinta ya kai mita 100, lokacin da ake sauka daga sama zuwa kasa, to za a iya saurarar wata babbar murya daga cikin hamada, wadda ta yi kamar muryar kararrawa.

Lokacin da na daga kai na ga hamada daga gindinta, na ga hamadar ta yi kamar wata magangarar ruwa, in an sauka daga sama zuwa kasa, to ya yi kamar ya sauka daga sararin sama, yana iya jin muryar kararrawa, ya iya jin dadin zama. Sabo da haka wurin ya zama daya daga cikin hamada hudu da ake iya saurarar murya a duk fadin kasar Sin.

A wurin Shapotou, ana iya ganin hanyar dogo ta farko ta kasar Sin wadda aka shimfida cikin hamada, wato hanyar dogo daga Baotou zuwa Lanzhou, kuma ana ganin cewa, wannan hanyar dogo wani abin al'ajabi ne na tarihin dan Adam wajen fama da hamada.

Sabo da an samu sakamako mai kyau wajen fama da hamada da kuma kiyaye muhalli, shi ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da wata lambar yabo ga wurin, wato "yankunan kiyaye muhallin halittu 500 mafi nagarta na duniya".