Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-06 16:40:08    
Kamfanin sarrafa magunguna na Jinyuyuan na jihar Ningxia

cri

Tare da saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin, rikicin rashin makamashi yana ta tsananta, sabo da haka yin amfani da abubuwa marasa amfani kamar yadda ya kamata zai zama wani muhimmin hanci ne wajen tabbatar da samun dauwamammen ci gaba a nan gaba, kuma raya tattalin arzikin bola jari zabi ne da ya zama wajibi wajen yin tsimin makamashi da kuma rage yawan abubuwan da ke gurbata muhalli da ake fitarwa.

Yau na je kamfanin sarrafa magunguna na Jinyuyan da ke birnin Qingtongxia na jihar Ningxia don yin intabiyu. Kamfanin yana kula da harkokin samar da magunguna kamar caustic soda da calcium carbide da dai sauransu, kuma abubuwa marasa amfani da wadannan magunguna ke samarwa suna iya gurbata muhallin halittu sosai.

Domin yin tsimin makamashi da kuma rage yawan abubuwan da ke gurbata muhalli da ake fitarwa, kamfanin ya kafa wani sashe na yin amfani da abubuwa marasa amfani wajen yin simiti a shekara ta 2003.

Lokacin da na shiga sashen samar da simiti na kamfanin Jinyuyuan, na gano cewa, wurin yana da tsabta sosai. Kuma wani babban injiniya ya gaya mini cewa, tun bayan shekara ta 2005, sashen ya riga ya yi amfani da abubuwa marasa amfani da nauyinsu ya kai fiye da ton dubu 300 wajen samar da siminti ton dubu 600. Kuma an riga an sayar da wadannan siminti zuwa jihohin Ningxia da Shanxi da Gansu da Mogolia ta gida da dai sauransu.

1 2