Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-03 19:10:03    
Lardin Jilin ya raya masana'antun da ke cikin hannun gwamnati bisa sabbin fasahohin da suka kirkiro da kansu

cri
Kamfanin nazarin fasahar bayani na Qiming mai hannun jari na daya daga cikin rukunin kera motoci na fako na kasar Sin mai hannun jari, wani kamfanin kera motoci mafi girma a kasar Sin da ke lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar. Bayan da aka kafa wannan kamfani, ya kara saurin yin nazari kan tsarin PDM, wato tsarin sa ido kan kayayyakin da aka kera. A shekarar 2001, kamfanin Qiming ya hada jami'o'i da hukumomin nazari ya yi shekaru 2 yana nazarin tsarin PDM, kuma ya samu nasarar fitar da tsarin PDM. Kamfanin Qiming yana da ikon mallakar wannan tsari. Ba ma kawai wannan tsari ya rage miliyoyin kudaden da kamfanonin kera motoci suke kashewa ba, har ma ya kawo wa kamfanin Qiming moriya da yawa. Mr. Cheng Chuanhai, babban direktan kamfanin Qiming ya bayyana cewa, "Idan wani kamfani yana son neman cigaba, dole ne ya kirkiro sabbin fasahohi da sabbin kayayyaki da kansa. Wannan yana da muhimmanci a gare kowane kamfani."

lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin muhimmin wuri ne da ke da masana'antu da yawa, musamman yana da dimbin masana'antun da ke cikin hannun gwamnati. Bayan da kasar Sin ta bayar da tsarin farfado da tattalin arzikin yankunan arewa maso gabashin kasar Sin a shekara ta 2003, wannan lardi ya kara saurin yin kwaskwarima kan masana'antu masu hannun jari da ke cikin hannun gwamnati, kuma ya sa kaimi kan wadannan masana'antu da su dogara da sabbin fasahohin da suka kirkiro da kansu lokacin da suke neman cigaba.

Kamar yadda kamfanin nazarin fasahar bayani na Qiming mai hannun jari yake yi, kamfanin yin magani na Tianyao na lardin Jilin ma yana neman bunkasuwa bisa sabbin fasahohin da ya kirkiro da kansa. An dade ba a iya yin amfani da dabarun sanya ido kan magungunan da sauran kasashen duniya suke bi ba lokacin da ake sanya ido kan ingancin magungunan gargajiya na kasar Sin. Sakamakon haka, sana'ar yin magungunan gargajiya na kasar Sin ba ta iya samun cigaba kamar yadda ya kamata ba, kuma ana samun wahala da yawa lokacin da ake shigar da magungunan gargajiya na kasar Sin a kasuwannin kasashen duniya. Sabo da haka, kamfanin yin magani na Tianyao ya yi kokari sosai wajen nazarin wata hanyar sanya ido kan magungunan gargajiya na kasar Sin da za ta iya samun amincewa daga kasashen waje. A shekara ta 2002, sabuwar hanyar sanya ido kan magungunan gargajiya na kasar Sin da wannan kamfani ya kirkiro ta jawo hankulan kwararru na kasar Sin da na kasashen waje sosai. Wannan sabuwar hanya ta samu amincewa daga sauran kasashen duniya. Game da cigaban da kamfanin ya samu, madam Qu Lianqing, direktan kamfanin yin magani na Tianyao ta ce, "Ina tsammani abin da ya fi muhimmanci shi ne dole ne a mai da hankali kan kirkiro sabbin fasahohi. Idan an kirkiro sabbin fasahohi, sana'o'in gargajiya ma za su iya samun cigaba a kasuwannin duniya. Kamfanin yin magani na Tianyao zai ci gaba da bin wannan hanya a nan gaba."

Shehun malami Li Dechang wanda yake nazarin sabbin fasahohi da dama ya taba ba da jagoranci ga kamfanin Qiming wajen kirkiro sabbin fasahohin da kamfani yake da ikon mallakarsu, ya ce, "Muddin kamfani ya mai da hankali kan kirkiro sabbin fasahohi da kansa, kamfani zai iya kawar da wahaloli iri iri lokacin da yake neman bunkasuwa. Yankunan arewa maso gabashin kasar Sin ma suna bukatar neman bunkasuwa bisa sabbin fasahohin da suka kirkiro da kansu."

A shekarar da muke ciki, gwamnatin lardin Jilin ta fitar da "ra'ayoyin raya sansanonin sabbin masana'antun da suke kirkiro sabbin fasahohi da kansu" domin sa kaimi kan kamfanoni da su kirkiro sabbin fasahohi domin neman cigaba. Yanzu wannan manufa tana taka rawa sosai. Tun daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar da muke ciki kawai, jimlar kudaden da aka samu daga masana'antun da ke kirkiro sabbin fasahohi da kansu ya kai fiye da kudin Renminbi yuan biliyan 250, wato ke nan ya karu da kashi 17 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. (Sanusi Chen)